Na fara garkuwa da mutane ne bayan an kashe miji na a Zamfara, in ji matar aure

Na fara garkuwa da mutane ne bayan an kashe miji na a Zamfara, in ji matar aure

- An kama wata mata yar asalin Zamfara da abokan aikin ta bisa zargin garkuwa a Jihar Kano

- Matar ta shaidawa yan sanda cewa ta shiga garkuwar ne bayan kashe mijin ta a Jihar Zamfara

- Ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ba kan lamarin har zuwa kammaluwar rahoton

'Yan sandan Jihar Kano sun kama wata mata mai garkuwa da mutane tare da wasu mutane biyu bisa zargin garkuwa da dan mai unguwar Galadanchi, Ado Sunusi, a karamar hukumar gwale da ke Kano, SaharaReporters ta ruwaito.

Bayan yan sandan sun bibiyu motar da aka sace yaron, sun kama direban motar a titin Beirut, a Kano.

Na fara satar mutane ne bayan an kashe miji na a Zamfara, matar aure
Na fara satar mutane ne bayan an kashe miji na a Zamfara, matar aure. Hoto: @daily_trust
Source: UGC

DUBA WANNAN: Bidiyo da Hotuna: Gobara ta tashi a babbar kasuwar Sokoto

Ta sanadiyar sa, aka gano inda matar ta ke, kuma aka gano ita ce uwar gayyar.

Hukumar yan sandan jihar ta bayyana cewa sun mamaye wani gida a unguwar Jaba da ke karamar hukumar Ungogo inda aka kama yan garkuwar da ake zargi.

An kama maza biyu da mace daya lokacin samamen, amma biyu daga ciki yan asalin Jihar Zamfara ne.

Bayan an gudanar da bincike, an gano cewa matar ta hayi gida a hannun wani mutum akan kudi 600,000 duk shekara, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Gwamnatin Trump ta kafa wani tarihi kwanaki biyu kafin sauka daga mulki

Matar ta shaidawa yan sanda cewa ta fara garkuwar ne bayan an kashe mijin ta a Zamfara.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, bai amsa kiran waya ko sakon kar ta kwana da wakilanmu suka aike masa ba har zuwa lokacin kammala rahoton.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel