Gwamnatin Trump ta kafa wani tarihi kwanaki biyu kafin sauka daga mulki

Gwamnatin Trump ta kafa wani tarihi kwanaki biyu kafin sauka daga mulki

- Gwamnatim Amurka karkashin Donald Trump ta kafa muhimmin tarihi bayan tsige shi a karo na biyu

- Mataimakin shugaban Kasar Amurka Mike Pence yayi ikirarin cewa gwamnati mai barin gado bata shiga sabon yaki ba

- Pence a wani bayani da ya wallafa a Twitter ranar Lahadi, 17 ga Janairu, yayi bayanin cewa wannan karo na farko cikin shekaru

Kasa da kwana biyu kafin karewar wa'adin Trump, gwamnatin mai barin gado ta ajiye tarihi.

A cewar mataimakin shugaban kasa Mike Pence, gwamnatin Trump ce ta farko cikin shekaru da bata jefa Kasar cikin yake yake ba.

Pence wanda ya bayyana haka a wani rubutu ta shafin Twitter ranar Lahadi, 17 ga Janairu, ya bayyana yadda ya ke alfahari da wannan gwamnatin.

DUBA WANNAN: Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ya mutu kwanaki 10 bayan rasuwar matarsa

Gwamnatin Trump ta kafa wani tarihi kwanaki biyu kafin sauka daga mulki
Gwamnatin Trump ta kafa wani tarihi kwanaki biyu kafin sauka daga mulki. Hoto: @Mike_Pence
Asali: Twitter

Ya wallafa:

"Ina alfaharin sanar daku cewa da yan kwanakin da suka rage mana a mulki, gwamnatin mu ce ta farko cikin shekaru da dama da bata jefa Amurka cikin sabon yaki ba. Wannan shi ne zaman lafiya cikin kwarin gwiwa".

KU KARANTA: An wajabtawa malamai da dalibai saka takunkumi bayan bude BUK

Sai dai, ikirarin mataimakin shugaban bai samu karbuwa wajen wasu yan Kasar Amurka ba yayin da suka kwakulo inda gwamnatin ta gaza.

A wasu ra'ayoyi da Legit.ng ta duba, 'yan adawa sun nuna yadda Trump ya fadi a yaki da annobar COVID-19.

@briantylercohen a shafin Twitter ya rubuta:

"Kuma yan Amurka za su mutu fiye da kowane yaki da kasar tayi fama dashi a tarihin Amurka."

@knotaboy yayi martani da cewa:

"A zance daga kayi gaskiya. Kun ki yakar annoba kuma mun cutu. Kun guji yaki (ba alamar karfi ba ne) kuma kun zo nan kun fara yakin. Babban birnin mu da mafi yawancin DC su ne sabbin Green Zone. Abin kunya. Akwai bukatar zama lafiya."

A wani labarin daban, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen Jihar Kebbi ta ce tana fatan za ta kwace mulki daga All Progressives Congress (APC) a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban jam'iyyar na jihar, Haruna Sa'idu, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin da ya ke tarbar jigo a jam'iyyar APC, Abdulmalik Halliru Milton, wadda ya fice daga APC ya koma PDP a Birnin Kebbi.

Sai'idu, ya kuma soki yan majalisar dokokin jihar da ya ce suna bari gwamnan Jihar Abubakar Atiku Bagudu na juya su duk yadda ya so.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel