Bidiyo da Hotuna: Gobara ta tashi a babbar kasuwar Sokoto
- Mummunan gobara ta tashi a babban kasuwa garin Sokoto
- Wutar da ta fara ci tun asubahi ta kone shaguna da dama
- Ma'aikatan kwana kwana da masu shaguna suna can suna kokarin kashe wutan
Gobara ta tashi a wani bangare na babbar kasuwar Sokoto misalin karfe 5 na asubahi na ranar Talata 19 ga watan Janairun 2020, TVC ta ruwaito.
Bidiyon gobarar ya nuna ma'aikatan kwana kwana, yan sanda da jami'an hukumar kiyayye haddura ta kasa, FRSC da wasu yan kasuwa na kokarin kashe gobarar.
Kawo yanzu ba a san anihin abinda ya yi sanadin afkuwar gobarar ba.
A halin yanzu ba a tabbatar ko gobarar ta yi sanadin rasa rayyuka ba.
DUBA WANNAN: Boko Haram ta fitar da bidiyon farfaganda na kwaikwayon atisayen sojoji
Kamar yadda ya ke a cikin bidiyon, dandazon al'umma sun taru wasu sun hau kan motocci suna kallon yadda ake kokarin kashe wutar.
Mahukunta su kan janyo hankulan mutane a kan yin takatsantsan da wuta musamman a irin wannan yanayi na bazara da iska ke kadawa sosai kuma mutane ke amfani da wuta don jin dumi.
Ga hotunan a kasa;
KU KARANTA: Gwamnatin Trump ta kafa wani tarihi kwanaki biyu kafin sauka daga mulki
A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.
Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng