Zababben shugaban karamar hukumar Bebeji, Ali Namadi, ya rasu

Zababben shugaban karamar hukumar Bebeji, Ali Namadi, ya rasu

- Allah ya yi wa zababen shugaban karamar hukumar Bebeji a Jihar Kano, Ali Namadi rasuwa

- Marigayin ya rasu ne misalain karfe daya na daren Litinin kwanaki biyu bayan hukumar zabe ta tabbatar masa da nasararsa

- Za a yi jana'izarasa a garinsu na Bebebji a ranar Talata kamar yadda mai magana da yawun tawagar yakin neman zabensa, Ibrahim Tiga ya sanar

Ali Namadi, wanda ya lashe zaben ranar Asabar na karamar hukumar Bebeji a Jihar Kano, ya riga mu gidan gaskiya, Daily Trust ta ruwaito.

Namadi ya rasu ne a ranar Talata misalin karfe daya na dare a cewa mai magana da yawun ofishin yakin neman zabensa, Ibrahim Tiga.

Zababen shugaban karamar hukumar Bebeji, Ali Namadi, ya rasu
Zababen shugaban karamar hukumar Bebeji, Ali Namadi, ya rasu. Hoto: @TVC News
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnatin Trump ta kafa wani tarihi kwanaki biyu kafin sauka daga mulki

An sanar da rasuwarsa a safiyar ranar Talata, kwanaki biyu bayan hukumar zabe na jihar ta tabbatar da nasararsa.

Kawo yanzu ba a sanar da sanadin mutuwarsa ba.

Namadi na cikin jerin 'yan takarar karamar hukuma na APC da suka yi nasara a zaben da aka kammala na kananan hukumomi a ranar 16 ga watan Janairun 2021 wadda har yanzu suna jirar rantsarwa.

KU KARANTA: Boko Haram ta fitar da bidiyon farfaganda na kwaikwayon atisayen sojoji

Za a yi jana'izarsa a garinsu na Bebeji a safyar ranar Talata, a cewar Tiga.

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel