Boko Haram ta fitar da bidiyon farfaganda na kwaikwayon atisayen sojoji

Boko Haram ta fitar da bidiyon farfaganda na kwaikwayon atisayen sojoji

- Mayakan kungiyar Boko Haram sun sake sakin sabon bidiyon farfaganda

- An cikin bidiyon an nuna yadda wani mai horaswa sanye da kayan sojoji ke basu horo mai kama da ta sojoji

- An yi magana da harsunan turanci, hausa da larabci a cikin bidiyon mai tsawon mintuna 17 da dakika 26

Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah Wa’l-Jihād da aka fi sani da Boko Haram a wani sabon bidiyon farfaganda da ta fitar a ranar Litinin ya nuna mambobinta na kwaikwayon atisayen sojoji da kai hari shingen sojoji, HumAngle ta ruwaito.

A cikin faifan bidiyon mai tsawon minti 17 da dakika 26 cikin harshen hausa, turanci da larabci ya nuna 'yan ta'addan suna atisayen sojoji da yadda ake koyon harbin bindiga.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Trump ta kafa wani tarihi kwanaki biyu kafin sauka daga mulki

Boko Haram sunyi bidiyo suna kwaikwayon atisayen sojoji
Boko Haram sunyi bidiyo suna kwaikwayon atisayen sojoji. Hoto: Hum Angle
Asali: Twitter

Boko Haram sunyi bidiyo suna kwaikwayon atisayen sojoji
Boko Haram sunyi bidiyo suna kwaikwayon atisayen sojoji. Hoto: Hum Angle
Asali: Twitter

Yan ta'addan sanye da kayan yaki mai launin ruwan kasa suna dauke da bindigun PKM, wadda ta yi kama da Zastava M21 da wasu samfuran Kalashnikov wadda aka saba amfani da su a yankunan Arewa maso gabas kusan shekaru goma da suka shude.

KU KARANTA: Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ya mutu kwanaki 10 bayan rasuwar matarsa

Boko Haram sunyi bidiyo suna kwaikwayon atisayen sojoji
Boko Haram sunyi bidiyo suna kwaikwayon atisayen sojoji. Hoto: Hum Angle
Asali: Twitter

Boko Haram sunyi bidiyo suna kwaikwayon atisayen sojoji
Boko Haram sunyi bidiyo suna kwaikwayon atisayen sojoji. Hoto: Hum Angle
Asali: Twitter

Ana iya ganin mai bada horaswa sanye da khaki irin ta sojoji wadda daga bisani ya yi magana da harshen turanci ya harba wata bindiga da ta yi kama da M-60 kirar Amurka.

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164