'Yan bindiga sun saki 'yan Nijar 9 a Jihar Katsina

'Yan bindiga sun saki 'yan Nijar 9 a Jihar Katsina

- Gwamnan Jihar Katsina ya bayyana sakin yan asalin Kasar Nijar 9 da aka yi garkuwa dasu a jihar bayan karbar su a gidan gwamnatin Jihar Katsina

- Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati da jami'an tsaro na iya kokarin su wajen ceto wanda aka yi garkuwa da su da kuma kawo karshen matsalar

- Gwamnan ya kuma karyata jita-jitar sulhu da yan ta'adda inda ya ce an sake su ne ba bisa wata yarjejeniya ba

An saki yan asalin Kasar Nijar 9 a Jihar Katsina, a cewar gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina.

Ya yi maganar ne bayan ya karbe su a gidan gwamnatin Jihar Katsina.

Ya ce an sake su bayan sa hannun al'umma ciki har da manyan jami'an tsaro.

Yan bindiga sun saki yan Nijar 9 a Jihar Katsina
Yan bindiga sun saki yan Nijar 9 a Jihar Katsina. Hoto: @daily_trust
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ya mutu kwanaki 10 bayan rasuwar matarsa

A cewar sa: "na gaya muku jami'an tsaro da gwamnatin Jihar Katsina na kokarin ceto wanda aka yi garkuwa da su a Jihar Katsina.

"Wancan lokacin mutane 144, ina Abuja karin 37 wanda aka tura su Jihar Zamfara saboda yan asalin jihar ne, sai kuma yau mun karbi mutum 9 wanda yan asalin jamhuriyyar Nijar ne.

"Gwamnati baza ta gaza ba a kokarin ta na ceto wanda aka yi garkuwa da su da kuma kawo karshen garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta'addanci a Jihar.

KU KARANTA: Buhari ya amince da nadin Nuhu Fikpo a matsayin shugaban riko na NDE

"Wanda aka yi garkuwa dasu da ayyukan ta'addanci yan garkuwa a Jihar Katsina zai zo karshe, ba iya Katsina ba har ma kasa baki daya."

Gwamnan ya karyata jita-jitar sulhu da yan bindiga "an sake su ne gaba daya ba tare da wata yarjejeniya ba."

A wani labarin daban, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen Jihar Kebbi ta ce tana fatan za ta kwace mulki daga All Progressives Congress (APC) a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban jam'iyyar na jihar, Haruna Sa'idu, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin da ya ke tarbar jigo a jam'iyyar APC, Abdulmalik Halliru Milton, wadda ya fice daga APC ya koma PDP a Birnin Kebbi.

Sai'idu, ya kuma soki yan majalisar dokokin jihar da ya ce suna bari gwamnan Jihar Abubakar Atiku Bagudu na juya su duk yadda ya so.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel