Jami'an Sojoji sun ragargaji yan bindiga a garin Birnin Gwari a jihar Kaduna
- An yiwa yan bindiga ruwan wuta a Birnin Gwari, Giwa, Igabi da Chikun
- An hallaka yan bindiga a garin Farin Ruwa da Kuduru dake karamar hukumar Birnin Gwari
- Gwamnan jihar Kaduna ya jinjinawa jami'an sojoji bisa jajircewansu
Rundunar Sojin Najeriya sun kashe wasu yan bindiga a harin da aka kai musu a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar.
Aruwan ya ce rundunar mayakan sama sun hallaka yan bindiga da dama kan baburansu a Saulawa, Kuduru da Farin Ruwa.
Ya ce mayakan sama sun kai hari wurare takwas a fadin jihar.
Bisa rahoton da gwamnatin jihar Kaduna ta samu, an kai harin leken asiri titin Kaduna-Abuka, Akilibu da Barebari.
Hakazalika an kai irin wannan hari Saulawa da Maguzawa, a cewarsa.
Ya kara da cewa da aka isa Farin Ruwa, an ga yan bindiga da dama kan baburansu inda aka bude musu wuta kuma aka kashe su.
Sauran wuraren da aka kai hari sune Riyawa Sarki, Sabon Gida Riyawa, Bunu, Hayin Maidawa, Buruku, Ungwan Yako, Kidandan, Dogon Dawa, Sabon Fili, Maguza, Damari da Ngede Allah.
Hakazalika an ga yan bindiga da shanu a hanyar Unguwan Yako zuwa Kudu kuma sojin sun bude musu wuta, Samuel Aruwan ya kara.
KU KARANTA: Kimanin mutane 2000 suka kamu cutar Coronavirus ranar Juma'a, mafi yawa tunda Korona ta bulla
KU DUBA: Haduran mota biyu sun yi sanadiyar mutuwar mutane 11 a jihar Edo
A wani labarin kuwa, rundunar jami'an Sojoji da jirgin yaki sun kawar da yan ta'addan ISWAP ada suka kai hari barikin sojoji dake Marte, jihar Borno.
An lalata motocin yaki da makamai yayinda sojojin suka kwace barikinsu da yan Boko Haram ta kwace.
Mutanen dake garin sun gudu daga muhallansu zuwa garin Dikwa.
Yan ta'addan ISWAP sun kai hari, da yammacin Juma'a, barikin Sojoji dake Borno, Arewa maso gabashin Najeriya, HumAngle ta ruwaito.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng