Yan ta'addan Boko Haram sun kwace barikin Sojoji dake Marte, Sojoji sun kwato abinsu

Yan ta'addan Boko Haram sun kwace barikin Sojoji dake Marte, Sojoji sun kwato abinsu

- Yayinda hukumar Soji ke ikirarin kawar da Boko Haram, yan ta'addan sun kwace wani barikin Soji

- Rahotanni sun bayyana cewa Sojin basu samu nasarar kwace barikinsu ba sai da Asabar

Rundunar jami'an Sojoji da jirgin yaki sun kawar da yan ta'addan ISWAP ada suka kai hari barikin sojoji dake Marte, jihar Borno.

An lalata motocin yaki da makamai yayinda sojojin suka kwace barikinsu da yan Boko Haram suka kwace.

Mutanen dake garin sun gudu daga muhallansu zuwa garin Dikwa.

Yan ta'addan ISWAP sun kai hari, da yammacin Juma'a, barikin Sojoji dake Borno, Arewa maso gabashin Najeriya, HumAngle ta ruwaito.

Rahoton ya nuna cewa har da safiyar Asabar suna cikin barikin.

Bayanan abubuwan da suka auku a harin dai basu bayyana ba har yanzu da ake kawo rahoton.

Wannan hari na zuwa ne lokacin da gwamnatin jihar Borno ke shirin mayar da mutane 300 garin.

A Oktoban 2020, gwamnan jihar ya kaddamar da kwamitoci biyu domin mayar da yan sansanin gudun Hijra Marte, Kirawa da Ngoshe.

Gwamnan na shirin mayar da su wajen ne saboda Marte gari ce na noma da kasuwanci.

Garin Marte ya shahara da noman Alkama.

Gwamnatin jihar a kwanakin baya na tattaunawar samar da wutan lantarki Marte da kewaye domin inganta noman zamani.

Gwamnan na haka ne domin rage adadin mutanen da zama a sansanin yan gudun hijra, hakazalika kuma domin noma, suna da kasuwancin da ke gudana a garin.

DUBA NAN: Kimanin mutane 2000 suka kamu cutar Coronavirus ranar Juma'a, mafi yawa tunda Korona ta bulla

Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari barikin Sojoji dake Marte
Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari barikin Sojoji dake Marte
Source: UGC

DUBA NAN: Zaben kananan hukumomi: 'Yan takara 6 sun fadi gwajin miyagun kwayoyi a Kano

A wani labarin kuwa, rundunar Sojin Najeriya sun kashe wasu yan bindiga a harin da aka kai musu a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Kwamishanan tsaro da harkokin cikin gidan, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar.

Aruwan ya ce rundunar mayakan sama sun hallaka yan bindiga da dama kan baburansu a Saulawa, Kuduru da Farin Ruwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel