Kimanin mutane 2000 suka kamu cutar Coronavirus ranar Juma'a, mafi yawa tunda Korona ta bulla

Kimanin mutane 2000 suka kamu cutar Coronavirus ranar Juma'a, mafi yawa tunda Korona ta bulla

- Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara

- Adadin wadanda suka kamu ranar Juma'a ya kafa sabon tarihi a Najeriya

- Har wa yau Najeriya bata sayo rigakafin Korona daga kasashen da suka samu ba

Da kimanin sabbin mutane 2,000 da suka kamu ranar Juma'a, Najeriya ta samu adadi mafi yawa a rana daya tun lokacin cutar Korona ta bulla a 2020.

Mutane 1,867 da aka tabbatar sun kamu da cutar a jihohi 23 da birnin tarayya, bisa rahoton da hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ranar Juma'a, 15 ga Junairy, 2021.

Kafin ranar Juma'a, adadi mafi yawa da aka samu shie ranar 6 ga Junairu inda mutane 1,664 suka kamu.

Daga cikin wadanda aka sallama ranar Juma'a, akwai mutane 277 da sukayi jinya a gidajensu a jihar Legas, mutane 150 a jihar Kaduna, mutane 78 a jihar Plateau, bisa ka'idar hukuma.

Amma an yi rashin mutane 8.

Adadin da aka samu ranar Juma'a ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 107,345 a Najeriya.

Daga cikin mutane kimanin 108,000 da suka kamu, an sallami 84,535 yayinda 1413 suka rigamu gidan gaskiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel