Haduran mota biyu sun yi sanadiyar mutuwar mutane 11 a jihar Edo

Haduran mota biyu sun yi sanadiyar mutuwar mutane 11 a jihar Edo

Juma'ar yau ba tayi kyau ba yayinda haduran mota biyu sukayi sanadiyar salwantan rayuka 15 a Arue-Uromi da Agbede.

Jaridar Punch ta ruwaito yadda kananan yara, mata da maza suka rasa rayukansu a jihar Edo.

Hadarin Arue-Uromi ya yi sanadiyar mutawan yara shiga; maza biyu da mata hudu, dukka yan gida daya.

Wata riwaya ta bayyana cewa yaran na tsallaka titi ne lokacin yayinda wata riwayar ta ce sun buga wasan kwallo ne wata mota kirar Marsandi ta bugesu.

An samu labarin cewa hakan ya fusata mutanen unguwar inda suka tare hanyar suka kona motar.

Sai kuma hadarin Agbede wanda ya faru tsakanin tankar mai, mota kirar Sienna da wasu motoci biyu.

Rayulan tara, mata takwas da maza daya suka salwanta.

Wasu fasinjoji a cikin mota sun jigata.

KU KARANTA: An fara yi wa mutane jabun rigakafin Korona

Haduran mota biyu sun yi sanadiyar mutuwar mutane 11 a jihar Edo
Haduran mota biyu sun yi sanadiyar mutuwar mutane 11 a jihar Edo
Asali: Original

KU KARANTA: Tantabarun da Buhari ya saki a bikin ranar tunawa da Sojoji sun ki tashi (Bidiyo)

Duka a ranar Juma'a, akalla mutane 15 sun rasa rayukansu a mumunan hadarin motar da ya auku tsakanin motocin Bas biyu a hanyar Maiduguri - Damaturu.

Sakta kwamandan hukumar FRSC, Sanusi Ibrahim, ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai (NAN) a Maiduguri.

Ibrahim ya ce hadarin ya faru ne kusa da garin Mainok, karamar hukumar Kaga a jihar Borno kuma an kai dukkan gawawwakin babban asibitin Benesheik, hedkwatan karamar hukumar.

"Yanzu na samu rahoto daga ofishinmu dake Benesheik cewa motocin bas kirar Sharon biyu sun yi kicibis kuma dukkan mutane 15 dake cikin motocin biyu sun mutu, " yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng