A hanyar Kogi, mutane 14 sun rasa rayukansu a hadarin mota ranar Alhamis
- Hadarin mota na kwasan rayukan yan Najeriya sabosa dalilai masu yawa
- Yayinda hanyoyi suka lalace, direbobi na wuce iyaka wajen gudu
- Wannan hadarin ya kwashi rayukan kananan yara har guda takwas
Akalla mutane 14 wanda ya hada da kananan yara biyar sun rasa rayukansu a hadarin motan da ya auku tsakanin motoci uku a hanyar Anyigba-Ajaokuta a jihar Kogi ranar Alhamis.
Hadarin ya auku tsakanin manyan motoci biyu da bas daya, Daily Trust ta ruwaito.
Ba'a gano takamammen abinda ya haddasa hadarin ba amma ana ganin lalacewan birkin daya daga cikin manyan motocin ne.
An samu labarin cewa mutane 14 cikin 23 da hadarin ya shafa sun mutu kai tsaye yayinda sauran mutane 9 suka jigata.
Sakta Kwamanda na hukumar FRSC, Solomon Aghure ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Lokoja.
Ya ce wadanda suka samu rauni an kaisu asibitin Holley Memorial dake Ochadamu domin jinya yayinda aka kai gawawwakin mamatan asibitin Grimard, Anyigba.
Aghure ya ce an kyautata zaton hadarin ya faru ne sakamakon lalacewar birki amma ana gudanar da bincike.
KU KARANTA: Tantabarun da Buhari ya saki a bikin ranar tunawa da Sojoji sun ki tashi (Bidiyo)
KU DUBA: An fara yi wa mutane jabun rigakafin Korona
A wani labarin mai alaka, akalla mutane 15 sun rasa rayukansu a mumunan hadarin motar da ya auku tsakanin motocin Bas biyu a hanyar Maiduguri - Damaturu ranar Juma'a, 15 ga Junairu.
Sakta kwamandan hukumar FRSC, Sanusi Ibrahim, ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai (NAN) a Maiduguri.
Ibrahim ya ce hadarin ya faru ne kusa da garin Mainok, karamar hukumar Kaga a jihar Borno kuma an kai dukkan gawawwakin babban asibitin Benesheik, hedkwatan karamar hukumar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng