Mutane 15 sun rasa rayukansu a mumunan hadarin da ya auku a Borno

Mutane 15 sun rasa rayukansu a mumunan hadarin da ya auku a Borno

- Hadarin mota na kwasan rayukan yan Najeriya sabosa dalilai masu yawa

- Yayinda hanyoyi suka lalace, direbobi na wuce iyaka wajen gudu

Akalla mutane 15 sun rasa rayukansu a mumunan hadarin motar da ya auku tsakanin motocin Bas biyu a hanyar Maiduguri - Damaturu ranar Juma'a, 15 ga Junairu.

Sakta kwamandan hukumar FRSC, Sanusi Ibrahim, ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai (NAN) a Maiduguri.

Ibrahim ya ce hadarin ya faru ne kusa da garin Mainok, karamar hukumar Kaga a jihar Borno kuma an kai dukkan gawawwakin babban asibitin Benesheik, hedkwatan karamar hukumar.

"Yanzu na samu rahoto daga ofishinmu dake Benesheik cewa motocin bas kirar Sharon biyu sun yi kicibis kuma dukkan mutane 15 dake cikin motocin biyu sun mutu, " yace.

"Hadarin ya shafi maza bakwai da mata takwas."

A cewarsa, Direban bas din ya yi batan hanya sakamakon fashewar tayar motarsa kuma hakan yayi sanadin karo da wata mota.

Ya yi kira ga direbobi su rika rage gudu domin ire-iren wadannan hadura.

KU KARANTA: Tantabarun da Buhari ya saki a bikin ranar tunawa da Sojoji sun ki tashi (Bidiyo)

Mutane 15 sun rasa rayukansu a mumunan hadarin da ya auku a Borno
Mutane 15 sun rasa rayukansu a mumunan hadarin da ya auku a Borno
Source: Facebook

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari na shirin sayar da dukiyoyin gwamnati don biyan albashi da ayyuka a 2021

A bangare guda, akalla mutane 14 wanda ya hada da kananan yara biyar sun rasa rayukansu a hadarin motan da ya auku tsakanin motoci uku a hanyar Anyigba-Ajaokuta a jihar Kogi ranar Alhamis.

Hadarin ya auku tsakanin manyan motoci biyu da bas daya, Daily Trust ta ruwaito.

Ba'a gano takamammen abinda ya haddasa hadarin ba amma ana ganin lalacewan birkin daya daga cikin manyan motocin ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel