Tantabarun da Buhari ya saki a bikin ranar tunawa da Sojoji sun ki tashi (Bidiyo)
- Wani abin mamaki ya faru yau a bikin ranar tunawa da sojojin Najeriya
- Ana wannan buki ne kowace ranar 15 ga Junairu a Najeriya
- A al'ada an san tantabaru da tashi idan suka samu dama, amma yau sun ki
Fararen tantabarun da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya saki a bikin ranar tunawa da jaruman Sojojin Najeriya sun ki tashi duk da yunkurin da shugaban kasan yayi.
Hakan ya janyo cece-kuce a kafafen ra'ayi da sada zumunta ranar Juma'a, 15 ga Junairu, 2021.
Sakin tantabarun wani al'ada ne da aka saba yi domin nuna cewa Najeriya na cikin zaman lafiya da lumana da kuma soyayyar juna.
Mai jagorantar bikin ya bayyana hakan yayinda shugaba Buhari ke kokarin ganin tantabarun sun tashi amma suka kiya.
Buhari ya bude kejin, ya dauki daya daga cikin tantabarun, ya jefa sama amma tantabarar ta dawo kuma taki tashi.
Bayan haka, Buhari ya bude kejin gaba daya domin dukkan tantabarun su tashi amma sukayi zamansu ciki yayinda wasu suka zauna a kan murfin kejin.
Shugaban kasan da ya gaji, sai ya hakura ya bar tantabarun kuma ya koma kujerarsa. Amma bayan wani lokaci da Buhari ya tafi, wasu cikin tantabarun suka tashi.
KU KARANTA; Abun bakin ciki yayinda Sultan na Sokoto ya rasa kaninsa Jeli
DUBA NAN: Yadda ranar 15 ga watan Junairun 1966 da 1970 suka canza tarihi har abada
Bincike ya nuna cewa tantabarun gida irin wadannan basu fiye damuwa da tashi ba.
Fafaroma Francis ya bada umurnin daina wannan al'ada a 2014 yayinda tantabaru biyu suka ki tashi a wani taro.
Hakazalika a 2014, tantabarun sun ki tashi lokacin da shugaba Goodluck Jonathan ya sake su.
Babban faston Adoration Ministry, Fada Mbaka, a lokacin yace wannan alama ce dake nuna Allah ba ya bayan Jonathan.
Yanzu haka mutane na tofa albarkatun yawunsu kan lamarin da ya auku yau Juma'a.
Ganewa kan ka bidiyon:
A bangare guda, shugabannin Najeriya fari daga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zuwa kasa sun halarci bikin ranar tunawa da jaruman Sojojin Najeriya da aka saba duk shekara.
Kamar yadda aka saba, an gudanar a bikin bana ne a farfajiyar Eagle Square dake kwaryar birnin tarayya Abuja.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila; da shugaba Alkalan Najeriya, Justice Muhammad Tanko.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng