Gwamnatin Buhari na shirin sayar da dukiyoyin gwamnati don biyan albashi da ayyuka a 2021
- Gwamnatin Buhari na neman hanyoyin samun kudi domin ayyuka a 2021
- Bayan basussuka da za ta karba daga gida da waje, ana shirin aron kudin ajiya a asusun bakunan yan Najeriya
- Hakazalika ana shirin sayar da wasu dukiya mallakar gwamnati
Bayan shirye-shiryen karban bashi domin biyan albashi da yin wasu ayyuka dake cikin kasafin kudin 2021, gwamnatin tarayya ta tabbatar da jita-jitan cewa za ta sayar da wasu dukiyoyin gwamnati yanzu.
Gwamnatin ya kara da cewa za'a yi amfani da wasu dukiyoyin da ba na man fetur ba domin daukan nauyin kasafin kudin 2021.
Hakan na kunshe cikin takardar da ministar kudi, Zainab Ahmed, ta gabatar ga masu ruwa da tsaki kan kasafin kudin 2021 da shugaban kasa ya rattafa hannu, Premium Times ta ruwaito.
A cewar takardar, daya daga cikin hanyoyin da za'a samo kudin amfani wajen biyan albashi da yin wasu ayyuka shine sayar da dukiyoyin gwamnati da kuma bada hayan wasu.
Ga hoton sashen takardar da ya nuan haka
Duk da cewa takardar bata bayyana dukiyoyin gwamnatin da za'a sayar ba, an samu tabbacin cewa lallai za'a sayar da wasu dukiyoyin yan Najeriya.
KU DUBA: Tantabarun da Buhari ya saki a bikin ranar tunawa da Sojoji sun ki tashi (Bidiyo)
KU KARANTA: An fara yi wa mutane jabun rigakafin Korona
Mun kawo muku cewa duk da rashin amincewar masu hannun jari, gwamnatin tarayya na shirin aron kudaden yan Najeriyan da ke asusun da aka dade ba'a waiwayesu ba, da kuma kudaden masu hannun jarin da aka dade ba'a bibiya ba.
Gwamnatin zata samu daman yin hakan ne bisa dokar kudin 2020 da shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu.
Karkashin sashe na 12 na dokar, an bayyana cewa za'a iya aron kudaden masu hannun jarin da ajiyan na mutanen wanda suka kai shekaru 6 ba'a waiwaya ba.
Gwamnati tace duk kudaden da ba'a bibiya ba za'a aika su wani asusun lamuni na musamman mai suna 'Unclaimed Funds Trust Fund'.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng