An bada belin sojan da ya caccaki yadda Buratai da Buhari ke tafiyar da yaki da Boko Haram

An bada belin sojan da ya caccaki yadda Buratai da Buhari ke tafiyar da yaki da Boko Haram

- An bawa sojan da ya yi bidiyo ya caccaki Shugaba Muhammadu Buhari da Buratai beli

- A cikin bidiyon, Idakpini Martins ya ce Shugaba Buhari da Manjo Janar Buratai ba su samarwa sojoji kayan yaki da Boko Haram isassu ba

- Daga bisani wani lauya mai rajin kare hakkin bil adama ya shigar da kara a madadin sojan kuma aka bada belinsa

Kotun sojoji da ke Jihar Sokoto ta bawa lance corporal Idakpini Martins beli bayan tsare shi na tsawon watnni bakwai da aka yi, News Wire ta ruwaito.

Lauyan sojan, Tope Akinyode, ya tabbatarwa Premium Times hakan cikin hirar da suka yi ta wayar tarho.

An bada belin sojan da ya caccaki yadda Buratai da Buhari ke tafiyar da yaki da Boko Haram
An bada belin sojan da ya caccaki yadda Buratai da Buhari ke tafiyar da yaki da Boko Haram. @NewsWire
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 2023: Matasa za su yi tattaki daga Legas zuwa Bauchi don neman gwamnan arewa ya yi takarar shugaban kasa

A 2020, Mista Martin ya wallafa bidiyo inda ya soki Shugaba Muhammadu Buhari da Babban hafsan sojojin kasa, Tukur Buratai saboda yadda suke tafiyar da yaki da yan Boko Haram.

Ya yi ikirain cewa su biyu sun gaza samarwa sojojin kayan aikin da za su yaki Boko Haram. An kama shi an kuma tsare shi a Abuja bayan fitowar bidiyon.

Ba a bawa Mr Martins damar ganin lauyansa ba tsawon wata daya sai bayan da Mista Akinyode, lauya mai kare hakkin bil adama ya tafi babban kotun Abuja ya shigar da karar keta hakkin bil adama a madadin Martins.

KU KARANTA: Kukah: FFK ya gargadi ƙungiyar musulmi kan kalamansu

Majiyar Legit.ng a ranar 22 ga watan Yulin 2020, ta ruwaito yadda Mai shari'a, A.I. Chikere ya bawa Martins daman ganin lauyansa da yan uwansa. Ya ce abinda rundunar sojin ta yi ya keta hakkin bil adama da dan kasa.

Bayan umurnin kotu, rundunar sojin bata bari ya ga yan uwansa ba kuma aka mayar da bincikensa zuwa Sokoto domin ya fuskanci hukunci tunda a nan ya aikata laifin da ake tuhumarsa da shi.

Mista Akinyode ya bayyana cewa na bawa sojan beli.

A wani labarin daban, lauyan Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, Ustaz Yunus Usman SAN a ranar Laraba ya tunkari kotu don janye karar da wanda ya ke karewa ya shigar.

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Alhaji Bashar wanda ya rasu ranar Juma'a, 1 ga Janairu, 2021, Daily Trust ta ruwaito.

Ustaz a wata tattaunawa ta wayar hannu da Daily Trust ranar Laraba ya ce ya bukaci janye karar wanda aka yi nan take.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel