Da duminsa: An nada kanin Kwankwaso matsayin sabon Makaman Karaye (Hotuna)

Da duminsa: An nada kanin Kwankwaso matsayin sabon Makaman Karaye (Hotuna)

- Gwamnan jihar Kano ya cika alkawari, ya maye gurbin kujeran Makaman Karaye da wani cikin iyalinsa

- Hakimin garin Kwankwaso, kanin Rabiu Musa, ya samu danewa kujeran

- Mai Martaba Sarkin Karaye ya yi masa nadin ranar Alhamis

Sarkin Karaye, Alhaji Ibrahim Abubakar II ya tabbatar da Alhaji Saleh Musa Saleh Kwankwaso (Baba) a matsayin Makaman Karaye kuma Hakimin Madobi.

Hakazalika ya zama mamban majalisar Sarkin Karaye kuma majalisar zaben sarki a masarautar Karaye.

A cewar Kakakin masarautar Karaye, Haruna Gunduwawa, an nada shi ne a ganawar majalisar sarkin Karaye da akayi ranar 13 ga Junaiiru 2021.

Yayin taya sabon Makaman murna, Sarkin Karaye ya yi kira da shi ya cigaba daga inda mahaifinsa ya tsaya.

Alhaji Saleh Musa Saleh Kwankwaso (Baba) wanda shine kanin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya gaji kujeran ne daga hannun mahaifinsa, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso.

An haifi Alhaji Saleh Musa a 1964, kuma ya nada Difloma a Injiniyancin gini.

Gabanin nadashi matsayin Makama, ya kasance Hakimin garin Kwankwaso a karamar hukumar Madobi.

Da duminsa: An nada kanin Kwankwaso matsayin sabon Makaman Karaye (Hotuna)
Da duminsa: An nada kanin Kwankwaso matsayin sabon Makaman Karaye (Hotuna) Hoto: Arewa Radio 93.1
Asali: Facebook

KU DUBA: Kuyi adalci wajen sukar da kukewa gwamnatina, Inji Buhari ga manyan kasa

Da duminsa: An nada kanin Kwankwaso matsayin sabon Makaman Karaye (Hotuna)
Da duminsa: An nada kanin Kwankwaso matsayin sabon Makaman Karaye (Hotuna) Hoto: Arewa Radio 93.1
Asali: Facebook

KU DUBA: Mun rabawa talakawa sama da 75,000 kudi N1.5bn a jihar Kebbi, Ministar Jinkai Sadiya Farouq

A ranar 9 ga Junairu, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyarar ta'aziyya wajen iyalan marigayi Makaman Karaye, mahaifin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, Alhaji Musa Sale Kwankwaso.

Ganduje ya jajantawa iyalan mamacin a gidansa dake garin Kwankwaso, karamar hukumar Madobi ta jihar.

Ganduje ya bayyana cewa: "Mun yi rashin mahaifi masu kula sosai. Allah ya jikansa kuma ya rahamshesa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel