Mun rabawa talakawa sama da 75,000 kudi N1.5bn a jihar Kebbi, Ministar Jinkai Sadiya Farouq

Mun rabawa talakawa sama da 75,000 kudi N1.5bn a jihar Kebbi, Ministar Jinkai Sadiya Farouq

- Gwamnatin tarayya ta bayyana irin biliyoyin kudin da ta rabawa mutane a Kebbi

- Gwamnati ta kara da cewa zata fara wani shirin rabawa mata N20,000

Ministar walwala da jin dadin jama'a, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa a shekaru biyar da suka gabata, gwamnatin tarayya ta kashe sama da bilyan 1.5 kan mutane jihar Kebbi.

Sadiya ta ce an rabawa talakawa marasa galihu 76,804 kudi N5000 kowani wata a jihar Kebbi.

Ministar wacce ta bayyana haka ranar Alhamis yayin kaddamar da wani sabon shirin rabawa yan matan karkara kudi a Birnin Kebbi, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarta, yan matan karkara 4,200 za su samu kudi N20,000 a jihar Kebbi inda tace za'a basu ne kyauta domin inganta rayuwar tattalin arzikin mata a jihar.

Ta kara da cewa an kaddamar da shirin ne tun Satumban 2016.

"Tun lokacin da aka kaddamar da shirin NSIP, jihar Kebbi ta samu jimillan kudi N1,056,200,000.00 daga gwamnatin tarayya kuma an inganta rayuwan talakawa 76,804," ta bayyana.

"Za'a rabawa matan Karkara 150,000 a jihohin tarayya kudi 36 da Abuja N20,000."

"Matan Karkara a nan jihar Kebbi 4,200 ne zasu amfana da wannan kudi N20,000."

A martanin gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Babale Umar Yauri, ya jinjinawa gwamnatin tarayya bisa wannan taimako.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Gwamnati ta yadda a bude makarantu

Mun rabawa talakawa sama da 75,000 kudi N1.5bn a jihar Kebbi, Ministar Jinkai Sadiya Farouq
Mun rabawa talakawa sama da 75,000 kudi N1.5bn a jihar Kebbi, Ministar Jinkai Sadiya Farouq Hoto: @Sadiya_Farouq
Asali: UGC

KU KARANTA: Sai bayan awanni 3 da muka kira yan sanda suka zo, shugaban APC da aka sacewa yara 7

A bangare guda, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya musamman manyan mutane da su yi adalci wajen sukar gwamnatinsa ta hanyar duba halin da kasar ke ciki kafin hawan gwamnatin yanzu, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis a fadar gwamnati da ke Abuja, yayin da ya karbi bakuncin Reverend Yakubu Pam, Sakatare Janar na Hukumar Alhazai ta Kiristocin Najeriya.

Shugaban ya ce: “Wadanda ke sukar gwamnatin ya kamata su yi adalci ta fuskar tunani a kan inda muke kafin mu zo, inda muke a yanzu da kuma irin kayan aikin da muka samu da kuma abin da muka yi da karancin kayan aiki."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng