Ganduje ya kai ziyara gidan Kwankwaso, ya yiwa iyalin babban alkawari

Ganduje ya kai ziyara gidan Kwankwaso, ya yiwa iyalin babban alkawari

- Gwamnan jihar Kano ya ajiye siyasa gefe, ya kai ziyara gidan mahaifin Kwankwaso

- Ganduje ya siffanta mahaifin Kwankwaso matsayin dattijo mai hakuri

- Ya yi alkawarin maye gurbin kujeran Makaman Karaye da wani cikin iyalinsa

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyarar ta'aziyya wajen iyalan marigayi Makaman Karaye, mahaifin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, Alhaji Musa Sale Kwankwaso.

Ganduje ya jajantawa iyalan mamacin a gidansa dake garin Kwankwaso, karamar hukumar Madobi ta jihar.

Gwamnan ya samu tarba daga kwamishanan raya karkara, Musa Ilyasu Kwankwaso, da kuma hakimin garin Kwankwaso, Alhaji Baba Musa Kwankwaso.

Ganduje ya bayyana cewa: "Mun yi rashin mahaifi masu kula sosai. Allah ya jikansa kuma ya rahamshesa."

Ya kara da cewa, "mahaifinmu mutumin kirki ne, mai hakuri ne, adili ne, kuma jajircacce. Shi yasa jama'ansa ke yabonsa. Allah ya gafarta masa kuma ya saka masa da Jannatul Fiddaus.”

Yayin bada masa kan bukatar da hakimin gari, kani ga tsohon gwamna Kwankwaso, kan Ganduje ya taimaka ya bar sarautar Madakin Karaye a dangin marigayin, Ganduje ya yi alkawarin cewa "Babu bukatar wannan, saboda gidan nan ya cancanci ko ma menene daga wajenmu. Ba zamu daina girmama gidan nan ba."

KU KARANTA: Sarkin Zazzau ya yi sabbin nade-nadensa na farko, ya yi sauye-sauye (jerinsu)

Ganduje ya kai ziyara gidan Kwankwaso, ya yiwa iyalin babban alkawari
Ganduje ya kai ziyara gidan Kwankwaso, ya yiwa iyalin babban alkawari Photo credits: @GovUmarGanduje, @KwankwasoRM
Asali: Twitter

KU DUBA: Tambari Yabo, tsohon mataimakin sufeto janar na yan sanda ya mutu

Makonni biyu kenan majidadin masarautar Karaye kuma hakimin karamar hukumar Madobi, Musa Saleh Kwankwaso, ya rasu yana da shekaru 93 a duniya.

Daily Nigerian ta rawaito cewa sakatare na musamman ga tsohon gwamna Kwankwaso, Mohammed Inuwa, ya tabbatar mata da rasuwar basaraken sakamakon takaitacciyar rashin lafiyar da ya yi a Kano.

An yi jana'izarsa ne a harabar masallacin gidan Rabiu Kwankwaso da ke unguwar Bompai a jihar Kano.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel