Bayan yi mata kyautan jego, maigida ya gano dan da matarsa ta haifa ba nasa bane

Bayan yi mata kyautan jego, maigida ya gano dan da matarsa ta haifa ba nasa bane

- Wani mutumi ya tayar da kura a sansanin Tuwita yayinda ya sanar da cewa da yiwuwan cikin shege matarsa ta haifa

- Mutumin mai suna @ceorashad ya bayyana da alamun damuwa da bakin ciki

- Tun lokacin da yayi maganar farko, ya cigaba da kananan maganganu da ke nuna halin kuncin da yake ciki

Wani mutumi a shafin Tuwita @ceorashad_ yanzu haka yana cikin bakin ciki da takaici yayinda ya gano da alamun matarsa ta yaudareshi game da sabon jaririn da ta haifa.

Mutumin ya bayyana shakkun kasancewar dan nasa ne.

A maganar da yayi ranar Laraba, 13 ga Junairu, mutumin yace ya gano da yiwuwan ba shine sahihin mahaifin yaron ba.

Abinda ya tayar da hankalin mutane shine ya nuna irin kyautan jakar hannu da kayayyaki masu tsadan da ya siya mata domin jego.

Bayan yi mata kyautan jego, maigida ya gano dan da matarsa ta haifa ba nasa bane
Bayan yi mata kyautan jego, maigida ya gano dan da matarsa ta haifa ba nasa bane source: @ceorashad
Source: Twitter

KU KARANTA: Cikin kwanaki 10, kimanin mutane 13,000 suka kamu da Korona

KU DUBA: Hadarin hanyar Bauchi ya yi sanadiyyar rayukan mutane 21 daga cikin fasinjoji 22 - FRSC

A wani labarin kuwa, wasu masoya 'yan kasar Ghana, wadanda suka kammala karatunsu a jami'a har suka samu ayyuka, sun tara N4,549,701.52 cikin shekaru 5 don yin hidimominsu.

Sun tattara tarin dukiyar ne don shagalin bikinsu, biyan kudin haya da kuma shagalin suna, bayan matar ta haihu.

Kamar yadda Chris Vincent na Ghanacelebrities.com, wanda yana da alaka da daya daga cikin masoyan, ya ce suna tsaka da soyayya sai budurwar ta samu juna-biyu. Read more:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel