Hadarin hanyar Bauchi ya yi sanadiyyar rayukan mutane 21 daga cikin fasinjoji 22 - FRSC

Hadarin hanyar Bauchi ya yi sanadiyyar rayukan mutane 21 daga cikin fasinjoji 22 - FRSC

- FRSC sun bayyana bayanan wadanda hadarin mota ya rufta dasu a hanyar Bauchi

- Hukumar ta fidda sunayen wasu mamatan da lambobin wayar wasu na kusa dasu

- A mutane 21 cikin 22 da hadarin ya rufta dasu suka mutu, yayin da daya ne ya tsira a galabaice

Yusuf Abdullahi, kwamandan reshen jihar Bauchi na Hukumar Kiyaye Haddura (FRSC), ya ce fasinjoji 21 daga cikin 22 da suka yi hatsarin mota a Bauchi sun mutu, Daily Trust ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Lahadi, lokacin da wata motar bas kirar Toyota Hummer ta Borno Express ta nufi Maiduguri daga Jos.

Motar tana dauke da fasinjoji 14 kuma ta yi karo ne da wata motar VW Golf 3 da ta zo daga Misau zuwa Bauchi, tare da Fasinjoji 8, ciki har da yara mata biyu.

KU KARANTA: Zulum ya ba da umarnin karin likitoci 40 aiki a asibitocin Borno

Hadarin hanyar Bauchi ya yi sanadiyyar rayukan mutane 21 daga cikin fasinjoji 22 - FRSC
Hadarin hanyar Bauchi ya yi sanadiyyar rayukan mutane 21 daga cikin fasinjoji 22 - FRSC Hoto: The Guardian
Source: UGC

Motocin biyu suna da lambobin rajista kamar haka: bas mai lamadBO89A28 da kuma Golf mai lamba MSA759XA.

Kimanin fasinjoji 22 ne hatsarin ya rutsa da su, biyu da farko sun tsira da munanan raunuka, yayin da suke karkashin kulawar Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (ATBU-TH), Bauchi.

Sai dai, shugaban FRSC, a wata hira da NAN a ranar Alhamis, ya ce daya daga cikin biyu da suka rayu shi ma ya mutu a ranar Litinin, yayin karbar magani.

“Wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, wadanda suka rasa rayukansu sun samu raunuka na daban kuma nan take suka mutu, yayin da wasu kuma suka kone ta yadda ba za a iya gane su ba.

“Jimillar mutanen da suka rasa rayukansu a hatsarin yanzu 21 ne.

"20 sun mutu a take daya kuma daga cikin biyu da suka rage shi ma ya mutu a ranar Litinin, yayin jinya," in ji shi.

Abdullahi, wanda ya ce gawarwakin dukkan mamatan an ajiye su a ATBU-TH, ya fitar da kwafin fasinjan motar bas din zuwa NAN da lambobin wayar wasu na kusa da wadanda suka mutu.

Ya ce dalili shi ne danginsu su san abin da ya faru su zo su karbi gawarwakinsu a asibiti.

Bayyanar kamar haka; lambar makusancin Mista Okoh Moses itace: 08062759179, Ishaq Hamzar: 07061555387, Success Dan Yarima mai lambar 08065696628 a matsayin na kusa, sai Babangida Hassan mai lambar 08030633003.

KU KARANTA: WHO ta dira Wuhan don bincike kan Korona

Sauran sun hada da, Palmala Haji mai lamba 08037313867, Christiana Pam mai lamba: 09061636896, Glory Jaka mai lamba 08035687986 da Yusuf Nadabo, 07039795511.

Kwamandan ya sake nanata cewa jami'ansu ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa masu bin hanyoyi sun bi duk dokokin kariya, don tabbatar da kare rayuka.

“Hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kan kudurinta na wayar da kan masu amfani da abin hawa a kan tuki lafiya da kuma bukatar bin ƙa'idodin zirga-zirga.

"Za mu ci gaba da gudanar da yakin wayar da kan jama'a a tashoshin mota, dandalin kasuwa da hanyoyi, kan hadari da dalilan da ke haifar da hatsarin hanya," in ji shi.

A wani labarin, Jerin gwano kanana da matsakaitan motoci, dauke da fasinjoji zuwa yankunan Kurna, Rijiyar Lemo da Bachirawa a wata tasha na wucin gadi da ake kira Tashar Buhari (Wurin Motar Buhari) ya zama shahararren wuri a jihar Kano.

Direbobin kananan motoci ne suka sanya wurin kaurin suna a jihar ta Kano.

Tashar motar, wanda aka fi sani da Tashar Buhari, ya sami sunanta ne saboda halin matsin tattalin arziki da kasar nan ke ciki a wannan gwamnatin ta Shugaba Muhammadu Buhari, Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel