Masoyan da suka adana N4.5m tsawon shekaru 5 sun hada shagalin bikinsu mai kayatarwa da kudin

Masoyan da suka adana N4.5m tsawon shekaru 5 sun hada shagalin bikinsu mai kayatarwa da kudin

- Wasu masoya da suka kammala karatunsu na jami'a, sun yi shekaru 5 suna ayyuka tukuru don ganin aurensu ya tabbata

- Cikin wannan lokacin, sun tara N4,549,701.52, ana tsaka da haka budurwar ta samu ciki, sai iyayensu suka bukaci su yi aure

- Sun yi amfani da dukiyar ne wurin shagalin biki, biyan kudin haya da kuma shagalin bikin suna bayan matar ta haihu

Wasu masoya 'yan kasar Ghana, wadanda suka kammala karatunsu a jami'a har suka samu ayyuka, sun tara N4,549,701.52 cikin shekaru 5 don yin hidimominsu.

Sun tattara tarin dukiyar ne don shagalin bikinsu, biyan kudin haya da kuma shagalin suna, bayan matar ta haihu.

Kamar yadda Chris Vincent na Ghanacelebrities.com, wanda yana da alaka da daya daga cikin masoyan, ya ce suna tsaka da soyayya sai budurwar ta samu juna-biyu.

Masoyan da suka adana N4.5m tsawon shekaru 5 sun hada shagalin bikinsu mai kayatarwa da kudin
Masoyan da suka adana N4.5m tsawon shekaru 5 sun hada shagalin bikinsu mai kayatarwa da kudin. Hoto daga YouTube
Asali: UGC

KU KARANTA: Mashahurin mai kudin duniya, Elon Musk, ya tafka asarar $14 biliyan a rana daya

Sakamakon yadda 'yan uwansu suka fara surutai, su na cewa wajibi ne su yi aure kafin cikin ya bayyana, dole tasa suka tattara kaf dukiyar da suka tara don amfani da ita.

Sun yi shagulgula daban-daban, tun daga shagalin gargajiya zuwa sauran shagulgula, inda suka yi amfani da 45,000GHs, sannan sun yi amfani da 15,000GHS don biyan kudin haya a Tema na shekara daya.

Bayan watanni 7 da yin bikin, sai matar ta haihu. Sun yi amfani da 10,000GHS, wanda yayi daidai da N649,957.36, wanda ya rage daga cikin kudin da suka tara don yin shagalin suna.

A cewar Chris, yanzu haka sun siya fili a Accra, kuma sun fara gina gida mai dakuna 2 da kudaden da suka tara.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kai hari kauyen Kaduna, sun halaka mutum 2

A wani labari na daban, wani mutumi daga yankin arewa maso gabas na kasar nan ya kalubalanci yadda ake tsawwala al'amuran aure a kasar Ibo.

A yayin da ya yi dogaro da wani lissafi tare da jerin kayan da ake bukata ango ya kaiwa dangin amarya a Nnewi na jihar Anambra, mutumin ya yi korafin ta shafinsa na Twitter.

Ya ce matasa a kasar Ibo suna shan wahala. Ya dace a rage yawan abubuwan da ake bukatar matashi ya kai idan yana neman aure.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: