Cikin kwanaki 10, kimanin mutane 13,000 suka kamu da Korona

Cikin kwanaki 10, kimanin mutane 13,000 suka kamu da Korona

- Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara

- Kwanaki 10 a jere, yan Najeriya sama da 1000 ke kamuwa da Korona kullum

- Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake kafa dokar hana fita idan adadin ya cigaba da karuwa

Mutane 1398 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Laraba, 14 ga watan Junairu 2021, kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Alhamis ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 103,999 a Najeriya.

Daga cikin mutanen da suka kamu, an sallami 8,555 yayinda 1382 suka rigamu gidan gaskiya.

Cikin kwanaki goma da suka gabata, kulli yaumin sai an samu akalla sabbin masu kamuwa 1000.

Kalli jerin addadin wadanda suka kamu tun ranar 4 ga Junairu zuwa 13 ga wata:

4 ga Junairu - Mutane 1204

5 ga Junairu - Mutane 1354

6 ga Junairu - Mutane 1664

7 ga Junairu - Mutane 1565

8 ga Junairu - Mutane 1544

9 ga Junairu - Mutane 1585

10 ga Junairu - Mutane 1024

11 ga Junairu - Mutane 1244

12 ga Junairu - Mutane 1270

13 ga Junairu - Mutane 1398

A jimilce, mutane 12,648 suka kamu da cutar kwanaki 10 da suka gabata.

KU KARANTA: Fitattun Farfesoshi 5 da Coronavirus ta hallaka

Cikin kwanaki 10, kimanin mutane 13,000 suka kamu da Korona
Cikin kwanaki 10, kimanin mutane 13,000 suka kamu da Korona Hoto: @NCDCgov
Asali: Twitter

KU DUBA: Kar a rufe jami’o’i har ba ranar bude su, Babalola ya fadawa FG

Ministar kudi da kasafin kudi, Zainab Ahmed Shamsuna, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kashe N118.37 billion annobar Korona kadai a shekarar 2020.

Ministar ta bayyana hakan ne yayin jawabi a taron bayani kan kasafin kudin 2021, ranar Talata, 12 ga Junairu, Vanguard ta ruwaito.

A cewarta, an kashe N10.08 trillion kan gine-gine, biyan basussuka, biyan albashi da fansho da kuma wasu cefane a 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel