Mun kashe kimanin N120bn kan Korona a 2020, gwamnatin tarayya
- Gwamnatin tarayya za ta kara tura bukatan wasu sabbin kudade cikin kasafin kudin 2021
- Ana bukatan hakan ne domin sayawa yan Najeriya rigakafin cutar Korona
- Za'a samo wadannan kudade na ta hanyar rantan kudaden yan Najeriya dake ajiye a bankuna
Ministar kudi da kasafin kudi, Zainab Ahmed Shamsuna, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kashe N118.37 billion annobar Korona kadai a shekarar 2020.
Ministar ta bayyana hakan ne yayin jawabi a taron bayani kan kasafin kudin 2021, ranar Talata, 12 ga Junairu, Vanguard ta ruwaito.
A cewarta, an kashe N10.08 trillion kan gine-gine, biyan basussuka, biyan albashi da fansho da kuma wasu cefane a 2020.
KU KARANTA: Dalibai sun fara barazanar dukan malaman jami'a idan basu koma makaranta ba
KU DUBA: Sabon kamfanin jiragen sama na Najeriya zai fara aiki
A wani labarin, masu kudaden dake ajiye a banki kuma suka dade basu waiwaya ba su kwantar da hankulansu saboda gwamnatin tarayya ta ce zasu iya cire kudadensu duk lokacin da suke bukata.
Ministar kudi, Hajiya Zainab Ahmed Shamsuna, ta bayyana hakan yayin amsa tambayoyi lokacin taron tattauna abubuwan da kasafin kudin 2021 ta kunsa jiya, Vanguard ta ruwaito.
"Za mu yi amfani da kudade da hannun jarin da ba'a waiwaya ba cikin wani asusu na musamman. Duk lokacin da banki ta tabbatar da mutum shine ainihin mai kusi, gwamnati za ta bashi," ministar ta bayyana.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng