Fitattun Farfesoshi 5 da Coronavirus ta hallaka

Fitattun Farfesoshi 5 da Coronavirus ta hallaka

Daya daga cikin manyan bangarorin da annobar korona ya girgiza a Najeriya shine fannin ilimi.

Baya ga tursasa wa dalibai zaman gida da mummunan annobar tayi sakamakon rufe jami’o’i da sauran makarantu da aka yi, ya kuma dauki rayukan manyan Farfesoshi.

KU KARANTA KUMA: Kukah: Jigon APC ya zargi JNI da kokarin hada rikicin addini, ya roki Buhari da Tambuwal su shiga lamarin

Najeriya ta rasa akalla Farfesoshi biyar sakamakon mummunan annobar.

Fitattun Farfesoshi 5 da Coronavirus ta hallaka
Fitattun Farfesoshi 5 da Coronavirus ta hallaka Hoto: @mrpirazzy, @OyoNews1, @ZankliC, @isnotpolitics, @SpeakerGbaja
Asali: Twitter

1. Farfesa Femi Odekunle

Femi Odekunle, mamba a kwamitin da ke ba shugaban kasa shawara a kan rashawa (PACAC) karkashin jagorancin Itse Sagay shima ya mutu sakamon COVID-19.

Odekunle farfesan shari’a ya mutu a yammacin ranar Talata, 29 ga watan Disamba, a cibiyar killace masu korona da ke Gwagwalada, Abuja.

KU KARANTA KUMA: Kalli jerin yan majalisan Republican 10 da suka yi watsi da jam’iyyarsu suka hade da Democrats wajen tsige Trump

2. Farfesa Lovett Lawson

A watan Yulin 2020, jaridar Punch ta ruwaito cewa wani farfasan da ya kamu da cutar, Lovett Lawson, ya mutu sakamakon cutar.

Lawson, wanda ya kasance daraktan cibiyar Zankli Medical Centre, Abuja, ya mutu a killace a asibitin kasa da ke Abuja.

3. Farfesa Oye Ibidapo-Obe

COVID-19 ta kuma dauki ran tsohon shugaban jami’ar Lagas, Farfesa Oye Ibidapo-Obe.

Farfesa Ibidapo-Obe har zuwa mutuwarsa ya kasance shugaban majalisar jami’ar fasaha na farko, Ibadan.

An tabbatar da mutuwarsa a cikin wata sanarwa daga sakataren majalisan, Olayinka Balogun a ranar 3 ga watan Janairu.

4. Farfesa Ebere Onwudiwe

Wani rahoto daga jaridar Premium Times ya nuna cewa Farfesa Ebere Onwudiwe, ya mutu sakamakon annobar korona a ranar 9 ga watan Janairu.

Baya ga mallakar digiri na uku kan kimiyar siyasa, ya kuma samu digiri na uku a fannin tattalin arziki da alakar kasa da kasa.

Ya riki mukamai daban daban a gida da wajen kasar, ciki harda aiki a matsayin farfesan kimiya a jami’ar tsakiya a Wilberforce, Ohio, inda ya zama darakta a cibiyar nazari na Afrika.

5. Farfesa Durojaiye Ajeyalemi

Farfesa Durojaiye Ajeyalemi, tsohon shugaban harkokin dalibai na jami’ar Lagas ne ya mutu sakamakon annobar korona.

Har zuwa mutuwarsa a ranar Laraba, 6 ga watan Janairu, Ajeyalemi ya kasance farfesan nazarin manhaja.

A wani labari na daban, wasu masu mugun nufi na yin furucin da ka iya tarwatsa kasar a cewar kungiyar dattawan arewa (NEF).

Musamman, kungiyar ta ce mutanen na yin zafafan kalamai a karkashin fakewa da addini.

Ta ce wadannan kalamai na iya haddasa fushi da tsoro a tsakanin al’umma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel