Babu wanda ya isa ya kori Bishop Kukah daga Sokoto, fadar shugaban kasa
- Fadar shugaban kasa ta kawo wa Rabaran Fada Matthew Kukah kariya
- Fadar Buharin ya ce duk da cewa Kukah ya fusata mutane, bai kamata a saba doka
- Bishop Matthew Kukah ya ce marabar gwamnatin Buhari da Boko Haram tayar da Bam
Fadar shugaban kasa ta yi tsokaci kan bukatar da wata kungiyar Musulmai a Sokoto ta yiwa Bishop Matthew Kukah cewa ya janye maganar da yayi ko kuma ya tattara inasa-inasa daga jihar Sokoto.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, yace wannan ba daidai bane kuma hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Garba Shehu ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Laraba mai taken, "Wajibi ne a rabu da Fada Kukah yayi addininsa da siyasarsa."
Shehu yace: "Rahoton da wata kungiya a Sokoto mai suna 'Kungiyar hadin kan Musulmai,' wacce ke kira ga Bishop na cocin Sokoto, Rabaran Matthew Kukah ya baiwa al'ummar Musulmai hakuri kan jawabinsa kan Musulunci ko ya fita daga jihar."
"Wannan ba daidai bane kuma ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya."
"Karkashin kundin tsarin mulkinmu, kowani dan Najeriya na da hakkin fadin abin da ya ga dama, ya mallaki abinda ya ga dama, kuma ya zauna duk inda ya ga dama a kasar nan ba tare da tsaiko ba."
KU KARANTA: Mun kashe kimanin N120bn kan Korona a 2020, gwamnatin tarayya
KARANTA WANNAN: Me suke so suyi? CAN ta dauki zafi yayinda kungiyar Musulunci ta nemi Kukah ya bar Sokoto
Mun kawo muku cewa babban faston darikar Katolika a kasar Sokoto, Mathew Hassan Kukah ya na fuskantar barazana bayan jawabinsa da ya yi na bikin kiremeti a 2020.
Kungiyar al’ummar Muslimi ta bukaci faston ya fito ya bada hakuri game da kalaman da ya yi, ta ce idan ba haka ba, ya yi gaggawa ya bar jihar Sokoto salin-alin.
Wata al’ummar musulmai da ke Sokoto sun fadawa Mathew Hassan Kukah ya daina sukar musulunci da kuma musulmai.
Wannan magana ta fito ne daga kungiyar Muslim Solidarity Forum ta reshen jihar Sokoto a wani jawabi da ta fitar ta bakin mukaddashin shugabanta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng