Me suke so suyi? CAN ta dauki zafi yayinda kungiyar Musulunci ta nemi Kukah ya bar Sokoto

Me suke so suyi? CAN ta dauki zafi yayinda kungiyar Musulunci ta nemi Kukah ya bar Sokoto

- Caccakar da ake yi wa Bishop Mattew Kukah ya dauki sabon salo

- Hakan na zuwa ne a lokacin da wata kungiyar Musulunci ta bukaci babban faston ya bar jihar Sokoto kan zargin kalaman tsokana

- Sai dai, a martaninta, kungiyar CAN ta ce shahararren faston ya yi magana ne bisa yancin da yake dashi a matsayinsa na dan Najeriya

Wata kungiyar al’umman Musulmi ta Muslim Solidarity Forum (MSF), ta bukaci Bishop Mattew Hassan Kukah da ya gaggauta barin Sokoto baki a leko kan kalaman tunzura da yayi.

Kungiyar ta yi barazanar a ranar Talata, 12 ga watan Janairu, a kan sukar gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shahararren malamin yayi, inda ta bayyana furucinsa a matsayin tsokana.

Legit.ng ta tuna cewa a cikin sakonsa na Kirsimeti a ranar Juma’a, 25 ga watan Disamba, Shugaban cocin Katolikan na Sokoto ya gabatar da cewa “babu wani shugaba da ba musulmi ba da zai yi abunda shugaba Buhari ke yi yaci lafiya.”

Me suke so suyi? CAN ta dauki zafi yayinda kungiyar Musulunci ta nemi Kukah ya bar Sokoto
Me suke so suyi? CAN ta dauki zafi yayinda kungiyar Musulunci ta nemi Kukah ya bar Sokoto Hoto: The Nation.
Source: UGC

Sukar da Kukah yayi ya zo ne a lokacin da ake tsaka da cece-kuce kannade-naden mukaman Shugaban kasar da halin da tsaron kasar ke ciki.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa 2023: Manyan Yarbawa 4 da ka iya hayewa kujerar Shugaba Buhari

Matsayar faston ya dade da haddasa cece-kuce daga daidaikun mutane da kuma addinai, koda dai ya ce an yi wa furucinsa bahagon fahimta ne a inda aka ce ya nemi a yi juyin mulki.

Ya kuma bayyana cewa ”shi ya fi damuwa da yadda za a yi amfani da addini wajen kawo hadin kai” yayinda ya kalubalanci kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta nuna inda ya ccaccaki Musulunci ko Musulmai a jawabinsa.

Amma a taron manema labarai a Sokoto, mukaddashin Shugaban MSF, reshen Sokoto, Isa Muhammad Maishanu, ya ce sakon malamin hari ne ga Musulunci kai tsaye, sannan yaa bukaci da ya bar jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kungiyar CAN ta yi martani

A halin da ake ciki, kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) ta yi martani ga kiran da aka yi na neman Kukah ya bayar da hakuri a kan furucinsa, inda ta bayyana barazanar MSF a matsayin abun dariya.

Babban sakataren kungiyar CAN, Rev. Joseph Daramola, yace shahararren faston ya yi magana ne bisa ka’idar yancin da yake da shi, jaridar This Day ta ruwaito.

“Me suke son yi masa? Shin za su hukunta shi ne? Za su maka shi a gaban kotu ne? Me zai sa shi bayar da hakuri? Shin suna da yanci? Ta yaya za ku bukaci tsarkakakken limamin katolika kamar wannan ya fito ya bayar da hakuri a kan ya fadi ra’ayinsa?”

A baya mun ji cewa, babban faston darikar Katolika a kasar Sokoto, Mathew Hassan Kukah ya na fuskantar barazana bayan jawabinsa da ya yi na bikin kiremeti a 2020.

Kungiyar al’ummar Muslimi ta bukaci faston ya fito ya bada hakuri game da kalaman da ya yi, ta ce idan ba haka ba, ya yi gaggawa ya bar jihar Sokoto salin-alin.

Wata al’ummar musulmai da ke Sokoto sun fadawa Mathew Hassan Kukah ya daina sukar musulunci da kuma musulmai, Punch ta fitar da wannan rahoto.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel