Da dumi dumi: Direbobi sun shiga zanga zanga a Lagos

Da dumi dumi: Direbobi sun shiga zanga zanga a Lagos

- Fasinjoji na shan wahala sakamakon zanga-zangar direbobin motocci ke yi a Jihar Lagos

- Direbobin sun tsunduma zanga-zangar ne saboda wasu kudade da hukumar harajin Jihar Lagos ta kakaba musu

- Wasu direbobin na dauke da makamai kuma suna farmakar duk wanda ya yi yunkurin daukar fasinja

Direbobin motoccin haya a Lagos a ranar Laraba sun shiga wata zanga-zanga sakamakon wani kudi da hukumar tara kudin shiga ta Jihar Lagos ta kakaba musu biya, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Zanga-zangar ta janyo cikowar fasinjoji daga Agege-Ogba-Berger na garin Lagos, ta kuma jefa fasinjoji cikin wahala inda wasu da dama cikinsu suka rika taka wa da kafafunsu zuwa wuraren da za su tafi.

Da dumi dumi: Direbobi sun shiga zanga zanga a Lagos
Da dumi dumi: Direbobi sun shiga zanga zanga a Lagos. @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Dukkanku dajin Sambisa za ku garzaya, Buratai ga sojin da ake horarwa

Zuwa karfe 12:14 na rana, lamarin tuni yayi kamarin da ya janyo wa fasinjoji tattaki mai nisa.

Wasu daga cikin direbobin sun rike makamai don tunkarar masu kame.

KU KARANTA: Sojoji 6 sun rasu sakamakon artabu da suka yi da 'yan bindiga a Katsina

Suna kuma kaiwa duk wani direba da ya yi yunkurin daukar fasinja hari.

Masu zanga-zangar sun rufe titin da ke sanannen mahadar Omole.

Kawo yanzu hukumar harajin ta jihar Legas bata bada ba'asi kan lamarin ba.

A wani labarin daban, kun ji kungiyar samari masu kishin aljihunsu da ake kira Stingy Men Association (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.

A ranar Litinin 11 ga watan Janairu ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Facebook tare da tamburi a Najeriya.

Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel