An rusa gidajen Dirama da Dambe guda 5 a Abuja

An rusa gidajen Dirama da Dambe guda 5 a Abuja

- Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara

- Kwanaki 9 a jere, yan Najeriya sama da 1000 ke kamuwa da Korona

- Hukumomi a birnin tarayya na hukunta wadanda ke saba dokar hana yaduwarta

Hukumar kula da birnin tarayya Abuja (FCTA) ta rusa gidajen dambe da dirama guda biyar bisa saba dokokin da gwamnati ta gindaya don dakile yaduwar cutar COVID-19 cikin al'umma.

Kwamitin yaki da cutar na birnin tarayya ta aiwatar da hakan ne a unguwar Daki-Biyu, Gwamrimpa da Sector Center inda aka damke mutane 25 kan laifin saba dokokin a cikin gari.

Jami'an yan sanda, jami'an DSS da jami'an NSCDC ne suka taimakawa kwamitin wajen wannan kame.

Yayin magana da manema labarai, shugaban kwamitin, Mr Ikharo Attah, ya ce an dade ana yiwa masu gidajen Dirama da Damben gargadin su daina budewa saboda ana saba dokokin kariya daga cutar Korona amma sukayi kunnen kashi, Daily Trust ta ruwaito.

"Dubunnan mutane na taruwa a wuraren shakatawan nan domin kallon mawaka da yan dambe, " yace.

"A daya daga cikin wuraren, mun gano cewa dubunnan mutane sun taru don kallon yan rawa. Babu takunkumin fuska, babu baiwa juna tazara kuma babu tsaftace hannu gaba daya".

Attah, ya yi kira ga yan wasan Kannywood dake zuwa wajen su daina.

"Idan muka kama su a wajen, zamu damkesu kuma mu gurfanar da su a kotu duk da shahararsu," yayi gargadi.

Bayan haka, an gurfanar da mutane 25, yawanci direbobi da fasinjoji kan laifin saba dokoki.

KU KARANTA: Dalibai sun fara barazanar dukan malaman jami'a idan basu koma makaranta ba

An rusa gidajen Dirama da Dambe guda 5 a Abuja
An rusa gidajen Dirama da Dambe guda 5 a Abuja
Asali: UGC

DUBA NAN: Yanzu yanzu: NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar SSCE

A wani labarin kuwa, gwamnatin jihar Kaduna ta gurfanar da sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, Abraham Alberah, da wasu mutane hudu kan zargin yunkurin aikata badala da shirya wata chasun badala da keta ka'idar COVID-19.

Alberah shine mijin Aisha Yakubu, mai Asher Lounge, wurin da aka shirya yin chasun Hukumar Birane da Tsare-tsare ta Jihar Kaduna ta rusa a ranar 31 ga Disamba, 2020.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta rusa ginin ne saboda aikata chasun badala amma daga baya ta juya zancen, inda ta bayyana cewa babban dalilin rusa ginin shi ne cewa ginin ba shi da lasisin gini.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel