Dalibai sun fara barazanar dukan malaman jami'a idan basu koma makaranta ba

Dalibai sun fara barazanar dukan malaman jami'a idan basu koma makaranta ba

- Gwamnatin tarayya ta ce za'a ita komawa karatu ranar 18 ga Junairu

- Ministan ilimi ya ce akwai yiwuwan za'a sake dage ranar komawar

- Kungiyar malaman jami'o'i ASUU ta cegaskiya bai kamata a bude makarantu ba

Shugabar jami'ar Benin (UNIBEN), Farfesa Lilian Salami, a ranar Laraba, ta ce a shirya suke da bude makarantu domin cigaba da karatu cikin kwanciyan hankali da lumana.

Farfesa Lilian ta bayyana cewa wasu dalibai sun fara yiwa malamansu barazanan bugu idan basu koma karantar da su ba.

Shugabar makarantar ta bayyana hakan ne yayin hira a shirin Good Morning Nigeria na tashar NTA.

Salami tace, "Ina son bayyana cewa shugabannin jami'o'i na da hankali saboda sun samu kwarewa a harkar karantarwa. Ba zai yiwu mu sanya rayuwar ma'aikatanmu cikin hadari ba, ko na dalibanmu ko kuma na wani daban."

"Muna jaddada cewa an bar jami'o'in gwamnati a baya. Babu kudi, babu kayan aiki, abubuwa sun lalace. Dalibai sun yiwa malamai yawa ta yadda za'a samu ingantaccen karantarwa, wajibi ne mu magance wadannan matsalolin."

DUBA NAN: NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar SSCE

Dalibai sun fara barazanar dukan malaman jami'a idan basu koma makaranta ba
Dalibai sun fara barazanar dukan malaman jami'a idan basu koma makaranta ba Hoto: Punch
Source: Twitter

KU KARANTA: Chasun Badala: Kaduna ta gurfanar da kakakin PDP tare da wasu da laifin yunkurin aikata badala

Malaman jami’a a ranar Litinin sun bayyana shirye-shiryensu na ci gaba da harkokin karatunsu a ranar Litinin mai zuwa kamar yadda Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta umurce su, The Nation ta ruwaito.

Malaman, sun roki Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar musu da lafiyar su da ta daliban su a yayin da ake kokarin shawo kan cutar ta COVID-19.

Shugaban Kungiyar Malaman Jami'o'in (ASUU), Farfesa Biodun Ogunyemi, ya ce tantancewar da rassanta suka yi ya nuna cewa mahukuntan jami'ar ba su yi abin da ya kamata ba don tabbatar da yanayin koyo mai inganci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel