Chasun Badala: Kaduna ta gurfanar da kakakin PDP tare da wasu da laifin yunkurin aikata badala

Chasun Badala: Kaduna ta gurfanar da kakakin PDP tare da wasu da laifin yunkurin aikata badala

- An gurfanar da wadanda suka shirya chasun badala a Kaduna ciki har da kakakin PDP

- Wadanda a ka kaman sun musanta zargin da ake musu yayin da kotu ta bada belinsu

- Kotu za ta ci gaba da sauraran karar ranar 20 ga watan Janairun 2020

Gwamnatin jihar Kaduna ta gurfanar da sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, Abraham Alberah, da wasu mutane hudu kan zargin yunkurin aikata badala da shirya wata chasun badala da keta ka'idar COVID-19.

Alberah shine mijin Aisha Yakubu, mai Asher Lounge, wurin da aka shirya yin chasun Hukumar Birane da Tsare-tsare ta Jihar Kaduna ta rusa a ranar 31 ga Disamba, 2020.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta rusa ginin ne saboda aikata chasun badala amma daga baya ta juya zancen, inda ta bayyana cewa babban dalilin rusa ginin shi ne cewa ginin ba shi da lasisin gini, The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA: Kotun Iraqi ta ba da sammacin damke Donald Trump

Chasun Badala: Kaduna ta gurfanar da kakakin PDP tare da wasu da laifin yunkurin aikata badala
Chasun Badala: Kaduna ta gurfanar da kakakin PDP tare da wasu da laifin yunkurin aikata badala Hota: African Studies Center
Asali: Facebook

Wadanda suka shirya chasun sun fada wa manema labarai cewa ba a yi chasun nuna badala ba kuma kawai shirme ne kawai don jawo hankalin masu halarta.

Mai otal din ta kuma zargi ‘yan sanda da karbar N120,000 daga hannunta wanda hakan ya sa ta rasa juna biyu.

Sai dai, a ranar Laraba, gwamnatin jihar ta gurfanar da wadanda ke kula da otal din, da ma'aikatan da ke aiki a wurin da kuma kwastomomin da suka shirya bikin.

A cewar takardar tuhumar, tuni a ka fara chasun badalar a ranar 27 ga Disamba, 2020, lokacin da ‘yan sanda suka isa wurin.

Wadanda ake tuhumar, da aka gabatar da su a gaban Kotun Majistare ta Gabasawa, an kuma zarge su da karya dokar COVID-19 da aikata lalata.

Laifin ya karanta a wani bangare, “keta dokar kulle na Gwamnatin Jihar Kaduna ta 2020, hada baki da aikata laifi da kokarin tada hankalin jama’a, badala ko kuma rashin da’a, babban lalata da badala.

“A ranar 27 ga Disamba, 2020 da misalin karfe 9:30 na yamma, an samu sahihan bayanai a ofishin‘ yan sanda na Sabon Tasha wanda ya nuna cewa wasu mutane da ba a san su ba ne suka shirya wani taron liyafa don gudanar da shi a wani wuri da ake kira Asher Guest Lounge da ke Titin Court, Sabon Tasha a Karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna za'a gudanar da kimanin karfe 7:00 na yamma.

“Bayan samun wannan bayanin, sai wasu 'yan sanda daga ofishin ‘yan sanda na Sabon Tasha suka garzaya zuwa wurin da aka ambata a sama kuma suka tarar da dakin da aka fada cike da matasa sama da 50 maza da mata suna rawa kusan ba kaya a jikinsu ba tare da wani abin rufe fuska ba.

KU KARANTA: El-Rufai ya saki N100m don yaran da ke fama da tamowa a Kaduna

“Da ganin ‘yan sanda, sai duk filin wasan ya rude kamar yadda matasan suka yi tsalle daga wannan kusurwa zuwa wancan suka tsere daga shingen. An kama mutane uku da ake zargi- Mista Abraham Alberah, Umar Rufa'i da Suleiman Lemona yayin da wasu biyu: Chimezie Kenneth, wanda ya shirya bikin da kuma Marvelus Akpan, wanda ya yada labarin. "

Mutanen da ake tuhumar sun musanta aikata laifin.

Alkalin kotun, Benjamin Nok, ya bayar da belin kowannensu N100, 000 tare da wanda zai tsaya masu da ya mallaki kadara a Abuja.

An daga shari’ar zuwa ranar 20 ga Janairun 2021, don ci gaba da shari’a.

A wani labarin daban, Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce ta kama wadanda suke shirya taron chasu na badala karo na farko a Jihar Kaduna, The Punch ta ruwaito.

Sai dai an soke yin biikin da ake shirya yi a ranar 27 ga watan Disambar shekarar 2020 duk da cewa ya yi suna a dandalin sada zumunta.

Daya daga cikin ka'idojin da masu shirya bikin suka saka shine mutane za su iso wurin ba tare da tufafi ba duk da cewa maza da mata ne za su hallarci chasun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel