Yadda makiyaya suka kashe manomi har lahira a Osun

Yadda makiyaya suka kashe manomi har lahira a Osun

-Wasu makiyaya sun kashe wani manomi a garin Osun a ranar Talata 12 ga watan Janairu

-Al'amarin ya faru ne a gonar manomin dake kauyen Boole

-Sai da shanun makiyayan suka lalata amfanin gonar marigayin kafin su kashe shi

Wasu makiyaya sun sheka wani manomi mai suna Ridwan har lahira bayan shanu sun lalata gonar marigayin kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Al'amarin ya faru ne a ranar Talata 12 ga watan Janairu.

An ruwaito cewa Ridwan wanda aka fi sani da Rado dan gidan Eesa a karamar hukumar Ijabe, Odo-Otin, jihar Osun, an kaimai harin ne a gonar shi dake kauyen Boole.

wani mazaunin garin, Oluwole Segun ya bayyana cewa shanun makiyayan sun lalata amfanin gonar marigayin bayan sun kaisu kiwo wurin, hakan tasa rikici ya barke tsakanin marigayin da daya daga cikin makiyayan.

"Ana cikin hakane makiyayin ya makure wa Ridwan wuya har lahira a take a wurin.

KU KARANTA-Matata tana kokarin ta kashe ni dan ta mallaki dukiyata: Magidanci ga Kotu

Yadda makiyaya suka kashe manomi har lahira a Osun
Yadda makiyaya suka kashe manomi har lahira a Osun Source: Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari ya yi alhini da juyayin mutuwar Hajiya Nafisatu Galadima Usman

"Wasu daga cikin matasa sun ruga a guje zuwa gidan makiyayan , inda suka kama wanda yayi aika aikan da wasu biyu da suke inda abun ya faru sannan suka garzaya dasu Police station dake garin.

Bayan nan yan sanda sun ziyarci inda abin ya faru, inda suka dauki gawar marigayin zuwa asibiti," A cewarsa.

Duk wani yunkuri na tuntubar kakakin hukumar yan sanda, Yamisi Opalola yaci tura domin numbar ta bata shiga. Amma wata kafa ta jami'an tsaro ta tabbatar da cewa an tura al'amarin zuwa ga hedikwatar tsaro domin cigaba da bincike.

A takaice, dattawa a yankin da abin ya faru sun gargadi matasa dasu daina daukan mataki da kansu, su rika barin hukuma tana aikinta.

Idan za ku tuna, Twitter ya rufe shafin Trump na tsawon sa'o'i 12, sannan aka goge wasu abubuwa da ya yada, a karshe aka shafe shafin na sa daga dandalin.

A dalilin gudun jawo tarzoma aka rufe shafin Donald Trump mai tarin mabiya kusa miliyan 90.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel