Buhari ya yi alhini da juyayin mutuwar Hajiya Nafisatu Galadima Usman

Buhari ya yi alhini da juyayin mutuwar Hajiya Nafisatu Galadima Usman

- Allah ya yi wa Hajiya Nafisatu Galadima Aminu Usman rasuwa, kamar yadda sanarwa daga fadar shugaban kasa ta nuna

- Marigayiya Hajiya Nafisa ta kasance babbar aminiya ga iyalin shugaban kasa, Muhammadu Buhari

- Hajiya Nafisa mata ce wurin Laftanal Kanal IG USman (mai ritaya) babban dogarin tsohon shugaban kasa Shehu Shagari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da uwargidansa, Aisha Buhari, sun yi alhini tare da juyayin mutuwar wata mai kusanci da su, Hajiya Nafisatu Galadima Aminu Usman.

Marigayiya Nafisatu mata ce wurin Laftanar Kanal IG Usman, dogarin tsohon shugaban kasa Shehu Shagari.

A cikin sakon da kakakinsa, Garba Shehu, ya fitar ranar Talata, Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga gidan sarautar Adamawa, gwamnatin jiha da kuma jama'ar jihar baki daya.

KARANTA: Rahama Sadau na fuskantar caccaka sakamakon sake sakin wani hoto a dandalin sada zumunta

Shugaba Buhari ya bayyana; "tsananin alhini da tausayawa a sakonsa na ta'aziyya" tare da bayyana Hajiya Nafisatu "a matsayin mace mai amana da bata taba nuna gajiyawa ba wajen bayar da goyon baya ga iyalin shugaban kasa."

Buhari ya yi alhini da juyayin mutuwar Hajiya Nafisat Usman
Buhari ya yi alhini da juyayin mutuwar Hajiya Nafisat Usman
Source: Facebook

KARANTA: Ahmed Musa ya sha nasiha da shawarwari bayan ya yada wani hotonsa da matarsa a dandalin sada zumunta

Shugaba Buhari ya yi addu'ar Allah ya jikanta ya kuma cigaba da tallafawa iyalinta da ta mutu ta bari, kamar yadda Garba Shehu ya sanar.

A baya Legit.ng Hausa ta rawaito cewa fadar shugaban kasa ta yi raddi tare da yi wa jam'iyyar adawa ta PDP kaca-kaca.

A wani jawabi da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, ya fitar, fadar shugaba kasa ta ce duk wani sauran tasiri da PDP keda shi ya kare saboda ta zama jami'ar karya, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

A cewar fafa shugaban kasa, jam'iyyar PDP ba ta yi komai ba a tsawon mulkinta na shekaru goma sha shidda bayan assasa cin hanci da rashawa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel