Matata tana kokarin ta kashe ni dan ta mallaki dukiyata: Magidanci ga Kotu

Matata tana kokarin ta kashe ni dan ta mallaki dukiyata: Magidanci ga Kotu

-Wani magidanci ya garzaya kotu akan a raba aurenshi da matarshi na shekara 12

-Ya bayyanawa kotu cewa matarshi na farautar rayuwarshi kuma tayi yunkurin kashe shi

-Mazaunin Ologuneru na a garin Oyo babbar birnin jihar Ibadan

Wani dan kasuwa mai suna Adeyinka Adeniyi ya garzaya kotun kustomary dake Ibadan ranar Talata, yana mai neman a raba aurenshi na shekara 12 kamar yadda daily trust ta ruwaito.

Magidancin ya bayyanawa Alkali cewa matarshi mai suna Elizabeth tana farautar rayuwarsa.

Adeniyi wanda mazaunin Ologuneru a garin Oyo ya siffanta matarshi da "Elizabeth sabuwar haifaffiyar shaidaniya ce."

"Babban gagarumin kuskuren da nayi a rayuwata shine auren Elizabeth. Ta sanya min guba tana yunkurin kashe ni."

"Ya mai shari'a' Ta sanya yan daba su kasheni a lokacin da gubar da ta sa min baiyi aiki ba," a cewar Adeniyi.

KU KARANTA: Abinda yasa mutane basu yarda da COVID-19 ba

Matata tana san ta kashe ni dan ta mallaki dukiyata: Magidanci ga Kotu
Matata tana san ta kashe ni dan ta mallaki dukiyata: Magidanci ga Kotu Source: Daily Trust
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta bada kwangilar dogo zuwa Nijar

A martaninta, Elizabeth ta musanta wasu daga cikin zargin.

Ta roki kotun ta bata ragamar kula da yayanta.

"Ya mai sharia'a Adeniyi ya dauke min yancina. Baya yarda yan uwana su ziyarce ni kuma baya biyan ma'aikatanshi albashinsu.

"Ya mai da ni da yayana biyu boyi boyinsa, muna mai aiki a mashayarsa ta hotel.Yana tilasta mana kwana muna aiki a hotel, "A cewar Elizabeth.

Shugaban kotun, Ademola Odunade, yace soyayyar dake tsakanin Adeniyi da Elizabeth ya gurbace.

Adumade ya tsinke igiyar auren.

Ya bar ragamar kula da babban dan ga Adeniyi shi kuma karamin ga Elizabeth.

Alkalin ya umurci Adeniyi daya rinka ba Elizabeth N5,000 duk wata na ciyar da yaran.

Dazu kun ji cewa NCDC ta fito ta ja-kunnen Jama’a bayan COVID-19 ta harbi mutane 100, 000.

Shugaban NCDC na kasa, Dr. Chikwe Ihekweazu ya ce cutar Coronavirus ta kai intaha a yanzu, ana gab da cike gadajen asibiti da masu jinya a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel