Twitter ta rufe shafin Trump, ta yi barazanar dakatar da shi har abada

Twitter ta rufe shafin Trump, ta yi barazanar dakatar da shi har abada

- Kamfanin Twitter ya rufe shafin Amurka, Donald Trump na tsawon awa 12 tare da goge wallafarsa uku

- Kamfanin ya yi hakan ne saboda a cewarta Shugaban na Amurka ya saba wasu dokokin amfani da shafin na sada zumunta

- Shugaban na Amurka ya wallafa sakonni na karfafa gwiwa ga magoya bayansa da suka yi kutse majalisar kasar da nufin dakatar da tabbatar da nasarar Joe Biden

Kamfanin sadarwa na manhajar Twitter ta rufe shafin Shugaba Donald Trump na Amurka saboda kalamensa a kan harin da aka kai Majalisar Amurka a ranar Laraba.

Trump, wadda har yanzu ya ki amincewa da kayen da ya sha a zaben da ta gabata da suka fafata da zabeben shugaban kasa Joe Biden, ya bukaci magoya bayansa suyi tattaki zuwa majalisa inda yan majalisar ke tabbatar da nasarar Biden a zaben ranar 3 ga watan Nuwamba.

Yanzu-yanzu: An rufe shafin Trump na Twitter, an yi barazanar dakatar da shi
Yanzu-yanzu: An rufe shafin Trump na Twitter, an yi barazanar dakatar da shi. Hoto: @thecableng
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Zaben kananan hukumomi: 'Yan takara 6 sun fadi gwajin miyagun kwayoyi a Kano

Masu zanga zangan sunyi tattaki zuwa majalisar inda suka nemi dakatar da shirin tabbatar da Biden.

Duk da cewa shugaban na Amurka ya bukaci magoya bayansa suyi zanga zangar lumana, ya karfafa musu gwiwa inda ya ce 'ba za a taba mantawa da abinda suka aikata a yau ba'.

Ya kuma harzuka su ta hanyar amfani da shafinsa na Twitter, inda ya rika yin wasu maganganu da ake ganin akwai kurakure cikinsa.

A martaninta, Twitter ta cire bidiyon da Trump ya wallafa inda ya bukaci masu zanga zangar su koma gida tare da jinjinawa abinda suka yi sannan yana sake maimaita ikirarin cewa an tafka masa magudi.

KU KARANTA: Tallafin Covid 19: 'Yan kasar Ghana za su sha wutar lantarki kyauta na watanni uku

Shafin na Twitter ya rufe shafin Trump sannan na tsawon awa 12 sannan ya cire wasu sakonni uku da ya wallafa.

"Sakamakon rikicin da ke faruwa a Washington D.C., an bukaci a cire wasu wallafa uku da @realDonaldTrump ya yi a yau na saba wasu dokokin mu," Twitter ta wallafa da shafinta na TwitterSafety.

Wannan shine mataki mafi tsauri da Twitter ta taba dauka game da shafin na shugaban kasar.

A wani labari na daban, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta bankado ayyukan almundahana a tallafin karatun kasashen waje na gwamnatin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar, Magaji Rimingado, wanda ya bayyana haka ga yan jarida ranar Talata, ya ce daga 2015 zuwa 4 ga Janairun 2021, gwamnatin jihar ta kashe naira biliyan 7 a tsarin wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata, amma ana samun korafin daliban da suka rage a kasashen waje.

Ganin yadda korafe korafe suka yi yawa kuma ya kamata ace da yawa yawancin daliban sun kammala karatun su, gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya umarci hukumar da tayi "bibiya", bincika ta kuma dauki mataki akan badakalar", in ji Rimingado.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel