Da duminsa: Sama da mutane 1500 sun kamu cutar Coronavirus ranar Alhamis

Da duminsa: Sama da mutane 1500 sun kamu cutar Coronavirus ranar Alhamis

- Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara

- Adadin wadanda suka kamu ranar Laraba ya kafa sabon tarihi a Najeriya

- Har wa yau Najeriya bata sayo rigakafin Korona daga kasashen da suka samu ba

Mutane 1565 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Alhamis, 7 ga watan Junairu 2021, kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Alhamis ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 95,934 a Najeriya.

Daga cikin mutane kimanin 96,000 da suka kamu, an sallami 77,982 yayinda 1330 suka rigamu gidan gaskiya.

Daga cikin wadanda aka sallama ranar Alhamis, akwai mutane 314 da sukayi jinya a gidajensu a jihar Legas, mutane 158 a jihar Kaduna, mutane 84 a jihar Plateau, bisa ka'idar hukuma.

Amma an yi rashin mutane 6.

KU KARANTA: EFCC ta ce za a hukunta yan Nigeria da suka siyar da lambobinsu na NIN

KU KARANTA: Za a yi jarrabawar 'kimiyyar shanu' ta kasar a India

A bangare guda, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karbi allurar rigakafin cutar COVID-19.

Ana ganin cewa shine dan Najeriya na farko da ya karbi rigakafin.

The Cable ta ruwaito mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya bayyana hakan ranar Alhamis.

Atiku ya yi nasa alluran ne a Dubai, hadaddiyar daular larabawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel