Da duminsa: Atiku ya zama dan Najeriyan farko da ya karbi allurar rigakafin Korona a Najeriya

Da duminsa: Atiku ya zama dan Najeriyan farko da ya karbi allurar rigakafin Korona a Najeriya

- Adadin wadanda suka kamu ranar Laraba ya kafa sabon tarihi a Najeriya

- A daidai lokacin tsohon dan takaran shugaban kasa ya karbi alluran rigakafi a kasar Dubai

- Ya bayyana muhimmancin rigakafin Korona ga al'ummar

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karbi allurar rigakafin cutar COVID-19.

Ana ganin cewa shine dan Najeriya na farko da ya karbi rigakafin.

The Cable ta ruwaito mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya bayyana hakan ranar Alhamis.

Atiku ya yi nasa alluran ne a Dubai, hadaddiyar daular larabawa.

"Muhimmancin rigakafin COVID-19 wajen dakile illar coronavirus abune wanda ba zamu gaji da jaddadawa ba, musamman a Afrika da Najeriya," mai magana da yawun Atiku ya bayyana.

"Jiya (Laraba) ya na cikin wadanda aka yiwa rigakafi, Atiku Abubakar ya karbi rigakafin Pfizer/Biontech."

"Ya kosa ya ga lokacin da yan Najeriya, musamman Likitoci masu faggen daga su fara karban nasu rigakafin."

KU KARANTA: Makonni 53 da bullar Korona: Abubuwa 8 da ya kamata ka sani

Da duminsa: Atiku ya zama dan Najeriyan farko da ya karbi allurar rigakafin Korona a Najeriya
Da duminsa: Atiku ya zama dan Najeriyan farko da ya karbi allurar rigakafin Korona a Najeriya Hoto: @thecable
Source: Twitter

DUBA NAN: Sabbin kamuwa da Korona: An samu adadin da ba'a taba samu ba a rana guda

A bangare guda, sa'anni kadan da suka shude majalisa ta tabbatar da nasarar Joe Biden a zaben shugabancin Amurka.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bi sahun tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Femi Fani-Kayode, wajen neman 'yan Najeriya su yi koyi da ka'idojin dimokuradiyya na Amurka.

Yana mai cewa 'manyan hukumomi masu karfin iko ba mutane masu karfin iko ba su ne tubalin kyawawan al'adun dimokiradiyya'.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel