EFCC ta ce za a hukunta yan Nigeria da suka siyar da lambobinsu na NIN

EFCC ta ce za a hukunta yan Nigeria da suka siyar da lambobinsu na NIN

- EFCC ta gargadi yan Najeriya a kan siyar da lambobinsu na yan kasa ba bisa ka’ida ba

- Hukumar yaki da rashawar ta bayyana dalilin da zai sa yan Najeriya su guji siyar da lambar su ta NIN

- Hukumar ta sanar da al’umma matakan da za su dauka idan aka tunkare su da batun siyar da lambobinsu na yan kasa

Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta yi gargadin cewa duk dan Najeriya da aka kama yana/tana siyar da lambarsa na yan kasa (NIN) na iya fuskantar tuhuma na ta’addanci.

EFCC ta yi gargadin ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Janairu, ta hannun kakakinta, Wilson Uwujaren, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Uwujaren ya bayyana cewa wasu marasa da’a sun rigada sun fara mika bukatar siyan lambar da kudi.

EFCC ta ce za a hukunta yan Nigeria da suka siyar da lambobinsu na NIN
EFCC ta ce za a hukunta yan Nigeria da suka siyar da lambobinsu na NIN HOTO: @nimc_ng
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Matashi ya bayyana yadda budurwarsa ta rabu da shi saboda ya ki fara 'Yahoo'

A cewar jaridar The Punch, kakakin na EFCC ya yi gargadin cewa mutanen da suka siyar da lambar NIN dinsu na iya tsintar kansu a cikin matsala idan aka alakanta shaidarsu na yan kasa da ayyukan ta’addanci.

Uwujaren ya ce:

“Wato a takaice, suna fuskantar barazanar kame su da hukunta su a kan duk wani aikin ta’addanci da lambar NIN dinsu ta fito imma suna da hannu ciki kai tsaye ko akasin haka."

Ya bukaci jama’a da su kai karar duk wani da ke neman siyan lambarsu ta NIN zuwa ofishin EFCC mafi kusanci ko sauran hukumomin tsaro.

A gefe guda, dubban mutane aka bari na shan sanyi a wajen ofisoshin hukumar katin dan kasa bayan ma'aikatan hukumar sun tsunduma yajin aiki, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Da zarar tattalin arziki ya dawo daidai, Ganduje zai koma biyan akalla N30, 600 a Kano

Sanarwar yajin aikin na dauke da sa hannun shugaban manyan ma'aikatan gwamnati, reshen hukumar NIMC, Lucky Michael, da sakataren ta, Odia Victor.

Hukumar sadarwar ta kasa ce dai ta umarci kamfanonin sadarwa da su datse duk wani layi da bai hada rijistar layin sa da lambar dan kasa ba kafin karshen Janairu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel