Za a yi jarrabawar 'kimiyyar shanu' ta kasar a India

Za a yi jarrabawar 'kimiyyar shanu' ta kasar a India

- Gwamnatin kasar India za ta gudanar da jarrabawa ta kasa kan 'kimiyyar shanu' da ake dauka abin bauta musamman ga Hindu

- Za a gudanar da jarrabawar ne don wayar da kan mutane tare da ilmantar da su kan darajar da shanu ke da shi

- Yara da manya har wadanda ba 'yan kasar ba za su iya yin jarrabawar sannan za a bada kyautuka da shaidar yin jarrabawa

- Kasar India na da dokoki da suka hana yanka shanu tare da tanadar hukunci daurin shekaru 7 ko tarar N5m a wasu yankunan kasar

Mahukunta a kasar India sun fara shirye-shirye domin jarrabawar 'kimiyyar shanu' da za a gudanar a kasar baki daya a wata mai zuwa.

Wannan shine yunkuri na baya-baya da gwamnatin Farai Minista Narendra Modi ta yi don habbaka da kare jinsin dabobin da mafi rinjaye na masu addinin Hindu ke dauka matsayin masu tsarki, Aljazeera ta ruwaito.

Za a yi jarabawar 'kimiyyar shanu' ta kasa a India
Za a yi jarabawar 'kimiyyar shanu' ta kasa a India. Hoto: Narinder Nanu/AFP
Asali: Twitter

Ana sa ran yin jarabawar na tsawon awa guda da za a yi ta yanar gizo ne a ranar 25 ga watan Fabrairu, kuma yara, manya har ma da wadanda ba 'yan kasa ba na iya yin jarrabawar.

KU KARANTA: Amsar Rahama Sadau game da batun dena fim bayan aure

Jarrabawar zai kunshi tambayoyi guda 100 a harsunan Hindi, Turanci da wasu harsuna 12 na yankunan da ke Asia.

A cewar Rashtriya Kamdhenu Aayog, Hukumar Kula da Shanu (RKA) da gwamnatin Modi ta kafa, an shirya jarrabawar ne domin gwada ilimin mutane da kuma 'wayar da kansu da ilmantar' da su.

"Za a bawa kowa satifiket na yin jarrabawar.

"Za a bada kyaututuka da shaidar karramawa ga wadanda suka nuna hazaka," a cewar Ma'aikatar Kifi, Kiwon Dabobi da Samar da amfani da Shanu a ranar Laraba.

"Shanu cike ya ke da kimiyya da tattalin arziki.

"Mutane ba su san ainihin muhimmanci da daraja a daba da ke shi ba ga kimiyya da tattalin arziki," in ji shugaban RKA Vallabhbhai Kathiria.

KU KARANTA: 'Yan majalisar Ghana sun bawa hammata iska kan batun rinjaye (Bidiyo)

RKA ta fitar da bayanai masu muhimmanci ga wadanda za su rubuta jarrabawar da suka hada da nau'in shanu da kuma batun cewa yanka dabobi na janyo girgizar kasa.

A manyan garuruwan da masu addinin Hindu suka fi rinjaye, shanu dabobi ne aka girmamawa domin alakanta su da bauta da ake yi.

Hukuma na iya hukunta mutum saboda yanka shanu a wasu yankunan kasar. A wasu wuraren kungiyoyin Hindu na kai wa Musulmi ko wasu Hindun wadanda aka yi wa kallon ba su da daraja hari.

A jihar Karnataka, yan sanda na iya kamawa tare da bincikar kowa kan zargin yanka shanu kuma ana iya yanke wa mutum hukuncin gidan yari na shekara 7 ko tarar rupees miliyan daya (N5,218,811).

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel