Harin Geidam: Yan Boko Haram sun yi awon gaba da Hakimi

Harin Geidam: Yan Boko Haram sun yi awon gaba da Hakimi

- Yan Boko sun hallaka mutane biyu, sun saci kayan abinci kuma sun kona dukiyoyin mutane

- Mazauna garin sun ce an dauke hakimin Geidam a harin

- Kakakin yan sanda ya ce sun tsinci gawawwaki biyu sun kone

Yan ta'addan Boko Haram sun yi awon gaba da hakimi a garin Geidam inda suka kai hari suna harbin kan mai uwa da wabi ranar Laraba, 6 ga watan Junairu, 2021.

Majiyoyi sun bayyana cewa yan ta'addan sun hari shaguna inda suka fasa suka kwashi kayan abinci sannan suka bankawa shagunan wuta.

Modu Ali, mazaunin garin ya bayyanawa manema labarai cewa bayan shagunan da suka yi fashin kayan masarufi kuma suka kona, sun kona gidan tsohon shugaban karamar hukumar, Dr Mulima Mato, The Nation ta ruwaito.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, ASP Dungus Abdulkarim, ya sanar da yan sanda cewa sun gano konanniyar mota kirar Hilux da gawawwaki biyu ciki amma basu sani ko yan Boko Haram bane ko yan gari.

Kakakin ya kara da cewa yan ta'addan sun je babban asibitin garin inda suka bukaci ma'aikatan su baiwa wasu daga cikinsu da suka ji rauni magani kafin suka gudu.

A cewarsa, yan ta'addan sun yi awon gaba da Hakimin garin Geidam.

Gwamnan jihar, Mai Mala Buni, ya umurci hukumar kai agaji na gaggawa ta jihar, SEMA, da ta kai dauki garin Geidam domin taimakawa wadanda harin ya shafa.

A jawabin da mai magana da yawunsa, Mamman Mohammed, ya saki, ya jajantawa al'umman garin Geidam.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari na shirin aron kudaden yan Najeriyan dake ajiye a banki

Harin Geidam: Yan Boko Haram sun yi awon gaba da Hakimi
Harin Geidam: Yan Boko Haram sun yi awon gaba da Hakimi
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zulum ya warewa mafarauta da CJTF N352m a Jihar Borno

Mun kawo muku rahoton cewa yan bindiga sun kai farmaki garin Geidam a jihar Yobe misalin karfe 6:30 na yammacin Laraba.

Harbe-harben ya tayar da hankalin mazauna garin kuma hakan ya sa suka gudu cikin daji yayinda wasu suka boye cikin gidajensu.

Kakakin hukumar yan sanda jihar, Abdulkarim Dungus, ya bayyana cewa ya tuntubi DPO na yankin lokacin suna artabu da yan ta'addan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel