Yanzu haka: Yan ta'addan Boko Haram na kan kai hari Geidam

Yanzu haka: Yan ta'addan Boko Haram na kan kai hari Geidam

- Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa ana artabu yanzu haka

- Wannan karon jihar Yobe yan ta'addan Boko Haram suka kai hari

Wasu yan bindiga da ake zargin yan Boko Haram ne sun kai farmaki Geidam, wani gari jihar Yobe da yammacin Laraba, 6 ga watan Junairu, 2021.

Yanzu haka misalin karfe 6:30 na yamma sun kan kai harin.

Harbe-harben ya tayar da hankalin mazauna garin kuma hakan ya sa suka gudu cikin daji yayinda wasu suka boye cikin gidajensu.

Yanzu haka: Yan ta'addan Boko Haram na kan kai hari Geidam
Yanzu haka: Yan ta'addan Boko Haram na kan kai hari Geidam
Source: Original

Jaridar Premium Times ta samu ji daga bakin wani a garin wanda ya bayyana halin da suke ciki.

"Harbe-harben da ake a waje yayi yawa. Ba zan iya magana ba yanzu," mazaunin ya laburta.

Kakakin hukumar yan sanda jihar, Abdulkarim Dungus, ya bayyana cewa ya tuntubi DPO na yankin lokacin suna artabu da yan ta'addan.

"Na kira DPO na Geidam kuma suna artabu. Ina jin karar bindigarsa. Ya yi alkawarin kiransa," Dungus ya bayyana.

Geidam mahaifar tsohon gwamnan jihar Yobe ne kuma Sanata mai ci yanzu, Ibrahim Geidam.

Garin na da nisam kilomita 200 da birnin jihar Damaturu kuma tana iyaka da jamhuriyyar Nijar.

Wannan ba shi ne karo na farko da yan Boko Haram ke kai hari garin ba.

KU DUBA: Gaskiya na gaji da boyewa, miji nike bukata - Kyakkyawar budurwa ta koka

A wani labarin kuwa, masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da matan Idris Mohammed, kansila mai wakiltar mazabar Gwako da ke Gwagwalada, guda biyu hade da karin wasu mutane uku a birnin tarayya Abuja.

Ba a bayyane sunan matan kansilan su biyu ba, kanwar sa mace da kuma kannen sa maza su biyu ba har yanzu.

Wani makwabci, wanda ya nemi a sakaya sunan shi, ya ce lamarin ya faru da misalin 12:08 na daren Litinin, lokacin da yan bindiga dauke da makamai suka yi wa gidan kansilan kawanya a kauyen.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel