Dan kwallon Super Eagles, Ahmed Musa, ya kaddamar da ginin katafaren makaranta a Jos

Dan kwallon Super Eagles, Ahmed Musa, ya kaddamar da ginin katafaren makaranta a Jos

- Babban dan kwallon Najeriya ya sake bayyana kudirin abin alheri

- Bayan taimakon da yake yiwa matasa na daukan nauyinsu a jami'o'i, zai gina sabuwar makaranta

Kyaftan na Super Eagles, Ahmed Musa, ya kaddamar da shirin ginin katafaren makaranta a Bukuru, karamar hukumar Jos South ta jihar Plateau saboda a wajen ya girma.

Ahmed Musa ya bayyana cewa zai gina makarantan ne matsayin mayar da alherin da garin tayi masa a matsayin mahaifarsa.

A sako mai kama da martani a shafinsa na Tuwita, Ahmed Musa, ya ce bai jahilci bukatar yin hakan ba.

"Ban jahilci bukatar mayar da alheri garina ba kuma dalilin haka ya sa nike farin cikin sanar da kaddamar da ginin makarantar M & S International School a jihar Plateau, karamar hukumar Jos ta kudu Bukuru," ya ce.

Dan kwallon Super Eagles, Ahmed Musa, ya kaddamar da ginin katafaren makaranta a Jos
Dan kwallon Super Eagles, Ahmed Musa, ya kaddamar da ginin katafaren makaranta a Jos Hoto: @Ahmedmusa718
Asali: Twitter

KU DUBA: 'Yan bindiga sun sace matar kansila da wasu mutane 3 a Abuja

Dan kwallon Super Eagles, Ahmed Musa, ya kaddamar da ginin katafaren makaranta a Jos
Dan kwallon Super Eagles, Ahmed Musa, ya kaddamar da ginin katafaren makaranta a Jos Hoto: @Ahmedmusa718
Asali: Twitter

Musa ya zama kyaftan din Super Eagles bayan John Obi Mikel yayi ritaya.

Ahmed Musa ya taka leda a kasashe irinsu Rasha, Holland, Ingila, da Saudiyya.

KU KARANTA: Gaskiya na gaji da boyewa, miji nike bukata - Kyakkyawar budurwa ta koka

A wani labarin kuwa, Ahmad Musa, ya bayyana shirinsa na bude wani katafaren flin wasanni a cikin birnin jihar Kaduna.

Tsohon dan wasan CSKA Moscow da Al Nasr na Sadiyya ya bayyana bidiyon wurin kuma da alamun an kusa kammalawa.

Wannan na zuwa ne shekaru biyu bayan wata daya bude a Kano, yayinda kuma ya bude shagon aski na alfarma bayan haka.

An gina filin ne a yalwataccen fili kuma za'a iya wasannin waje da na kulle.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng