Ahmed Musa na shirin bude katafaren filin wasa a Kaduna (Bidiyo)

Ahmed Musa na shirin bude katafaren filin wasa a Kaduna (Bidiyo)

- Kyaftin na yan kwallon Najeriya, Super Eagles, Ahmed Musa na gab da bude cibiyar wasanni a Kaduna

- Tsohon jarumin kungiyar Leicester ya bayyana hakan a kafar sada zumunta

- Tuni Musa ya bude wani cibiyar a Kano shekaru biyu da suka shude, sannan shagon aski

Babban dan kwallon Super Eagles, Ahmad Musa, ya bayyana shirinsa na bude wani katafaren flin wasanni a cikin birnin jihar Kaduna.

Tsohon dan wasan CSKA Moscow da Al Nasr na Sadiyya ya bayyana bidiyon wurin kuma da alamun an kusa kammalawa.

Wannan na zuwa ne shekaru biyu bayan wata daya bude a Kano, yayinda kuma ya bude shagon aski na alfarma bayan haka.

An gina filin ne a yalwataccen fili kuma za'a iya wasannin waje da na kulle.

Duk da cewa bidiyon bai nuna irin kayayyakin dake cikin cibiyar ba, ana kyautata zaton akwai kayayyakin motsa jikin zamani da sauransu.

Musa, ya ce za'a bude cibiyar wasannin nan ba da dadewa ba amma bai bayyana takamammen lokacin ba.

KU DUBA: Idan iyayenka sun haifeka dan Halas, ka shigo Zamfara kai kadai: Matawalle ga Yari

Ahmed Musa na shirin bude katafaren filin wasa a Kaduna (Bidiyo)
Ahmed Musa na shirin bude katafaren filin wasa a Kaduna (Bidiyo) Hoto: @NGSuperEagles
Asali: Twitter

DUBA NAN: Karya ne, bamu baiwa Ganduje Farfesa ba, jami'ar East Carolina

A baya muna kawo muku cewa Ahmed Musa ya karyata rahoton komawa taka leda a kungiyar kwallon Sheffield dake Ingila.

Dan shekara 28 din ya raba jiha da kungiyar Al Nassr na Saudiya.

A Yunin 2017, Musa ya bude cibiyar wasanni a jiharsa ta Kano inda aka ce yayi hakan ne don rashin wurin wasanni a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng