Gaskiya na gaji da boyewa, miji nike bukata - Kyakkyawar budurwa ta koka

Gaskiya na gaji da boyewa, miji nike bukata - Kyakkyawar budurwa ta koka

- Wata kyakkyawar budurwa mai suna Maryam a Twitter, ta yi ta maza

- Kyakkyawar budurwar yar Gombe ta shiga Twitter neman miji

- Ta bukaci jama’a su taimaka mata da addu’a saboda ta gaji da boyewa

Wata kyakkyawar budurwar mai suna Maryam a manhajar Tuwita ta yanke shawarar bayyanawa duniya yadda take ji a zuciyarta saboda gaskiya ta gaji da boyewa.

Maryam ta shiga Tuwita don bayyana ra’ayinta na neman miji saboda ta gaji da boyewa.

A shekarun baya-bayan nan, kafafen ra’ayi da sada zumunta sun taimaka matuka wajen hada samari da yan mata masu neman aure.

Maryam ta ce gaskiya ta gaji da boye yadda take ji kuma tana bukatan miji.

Ta kara da cewa ita yar jihar Gombe ce kuma jama’a su taimaka mata da addu’a.

Gaskiya na gaji da boyewa, miji nike bukata - Kyakkyawar budurwa ta koka
Gaskiya na gaji da boyewa, miji nike bukata - Kyakkyawar budurwa ta koka Hoto: @ MQueeniee33
Asali: Twitter

KU KARANTA: Makonni 53 da bullar Korona: Abubuwa 8 da ya kamata ka sani

KU DUBA: ASUU: 2020 ta wuce ba a biya EAA ba, an hana Malamai albashin watan Disamba

A wani labarin kuwa, wani bidiyo da ya yadu a kasar Pakistan wanda ke nuna daurin aure tsakanin wani mutumi da sabuwar amaryarsa ya janyo cece-kuce a kafafen ra'ayi da sada zumunta.

Netizens da kafafen yada labarai a Pakistan sun bayyana cewa matar da aka gani cikin bidiyon wata hamshakiyar attajira ce yar kasar Saudiyya, Sahoo bint Abdullah Al-Mahboud, yayinda kuma mijin da ta aura direbanta ne.

Bincike ya nuna cewa lallai matar itace Sahoo wacce ke da mallakin dukiyoyi a fadin duniya musamman Makkah, Madina, da kasar Faransa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel