Kungiyar manyan ma'aikatan Poly a Najeriya sun shiga yajin aiki

Kungiyar manyan ma'aikatan Poly a Najeriya sun shiga yajin aiki

- Yayinda ake -cewa kungiyar ASUU za ta iya komawa wani sabon yajin-aiki, na Poly sun shiga

- Sun gargadi gwamnatin tarayya cewa idan ba'a amsa bukatansu ba, zasu tafi na din-din-din

- Jihohi da dama sun sanar da ranakun bude makarantu bayan hutun Kirismeti da sabon shekara

Manyan ma'aikatan kwalejin fasaha (poly) a fadin Najeriya, (SSANIP), sun kaddamar da yajin aikin gargadi a fadin tarayya kan rashin biyan bukatunsu da gwamnatin tarayya tayi.

A ganawar shugabannin kungiyar ma'aikatan, an gargadi gwamnatin tarayya cewa idan bata biya bukatun ma'aikata ba, mambobin kungiyar zasu shiga wani yajin aikin gaba daya.

Shugaban SSANIP na kasa, Philip Ogunsipe, ya ce sama da shekaru 10 kenan ana yarjejeniya kuma har yanzu ba'a cimma matsaya ba.

Philip Ogunsipe, ya ce gwamnatin tarayya na cigaba da yiwa lamarin rikon sakainar kashi, hakan ya sa suka yanke shawarar shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 14.

Shugabannin SSANIP na kwalejin fasaha daban-daban a fadin tarayya sun yi amanna da wannan hukunci da uwar kungiyar ta yanke kuma tuni sun kaddamar da yajin aikin.

Daga cikin wadanda suka tabbatar da hakan akwai shugaban SSANIP na kwalejin fasahar Legas, Oluseye Ero-Philips; shugaban SSANIP na kwalejin fasahar Ede, Emmanuel Oyeyode; shugaban SSANIP na kwalejin fasahar Offa, Oyinlola Abdulmajeed; da shugaban SSANIP na kwalejin fasahar Nekede, Christian Ononogo.

KU KARANTA: Hamshakiyar attajira, Sahoo Bint Abdullah Al-Mahboub, ta auri direbanta (Bidiyo)

Kungiyar manyan ma'aikatan Poly a Najeriya sun shiga yajin aiki
Kungiyar manyan ma'aikatan Poly a Najeriya sun shiga yajin aiki Hoto: Kadpoly
Asali: UGC

KU DUBA: Gaskiya na gaji da boyewa, miji nike bukata - Kyakkyawar budurwa ta koka

A bangare guda, rahotanni sun bayyana cewa kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta fara maganar komawa yajin-aikin da ta dakatar a watan Disamban 2020.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, 5 ga watan Junairu, 2020 wanda ya nuna cewa kungiyar ASUU tana barazanar tafiya yajin-aiki.

Hakan na zuwa ne kwanaki 13 bayan malaman jami’an sun amince su janye yajin-aikin da su ka shafe tsawon watanni kusan tara suna yi a kasar.

Dama can ASUU ta bada sharadi cewa muddin gwamnatin tarayya ba ta cika alkawuran da ta dauka ba, ba za su ji kyashin komawa yajin-aiki ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel