Hamshakiyar attajira, Sahoo Bint Abdullah Al-Mahboub, ta auri direbanta (Bidiyo)
- Wani direban mota ya canki babban rabo yayinda ya auri matar da yake tukawa
- Sahoo bin Abdullah hamshakiyar attajira ce kuma yar kasar Saudiyya
- Auren yar Saudiyya ko da kudinka sai ka sha da kyar
Wani bidiyo da ya yadu a kasar Pakistan wanda ke nuna daurin aure tsakanin wani mutumi da sabuwar amaryarsa ya janyo cece-kuce a kafafen ra'ayi da sada zumunta.
Netizens da kafafen yada labarai a Pakistan sun bayyana cewa matar da aka gani cikin bidiyon wata hamshakiyar attajira ce yar kasar Saudiyya, Sahoo bint Abdullah Al-Mahboud, yayinda kuma mijin da ta aura direbanta ne.
Bincike ya nuna cewa lallai matar itace Sahoo wacce ke da mallakin dukiyoyi a fadin duniya musamman Makkah, Madina, da kasar Faransa.
Hakazalika an yi kiyasin cewa arzikinta ya kai dala biyan takwas ($8bn).
KU KARANTA: Kanin mataimakin gwamnan Jihar Legas ya rasuwa bayan kamuwa da korona
KU KARANTA: Makonni 53 da bullar Korona: Abubuwa 8 da ya kamata ka sani
A wani labarin mai alaka, wata kyakkyawar budurwar mai suna Maryam a manhajar Tuwita ta yanke shawarar bayyanawa duniya yadda take ji a zuciyarta saboda gaskiya ta gaji da boyewa.
Maryam ta shiga Tuwita don bayyana ra’ayinta na neman miji saboda ta gaji da boyewa.
A shekarun baya-bayan nan, kafafen ra’ayi da sada zumunta sun taimaka matuka wajen hada samari da yan mata masu neman aure.
Maryam ta ce gaskiya ta gaji da boye yadda take ji kuma tana bukatan miji.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng