ASUU: 2020 ta wuce ba a biya EAA ba, an hana Malamai albashin watan Disamba

ASUU: 2020 ta wuce ba a biya EAA ba, an hana Malamai albashin watan Disamba

- Ana rade-radin cewa kungiyar ASUU za ta iya komawa wani sabon yajin-aiki

- Gwamnati tayi alkawarin biyan Malamai alawus zuwa ranar 31 na watan jiya

- An shiga 2021 ba a biya EAA ba, sannan an ki biyan Malaman albashin Disamba

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta fara maganar komawa yajin-aikin da ta dakatar a watan Disamban 2020.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, 5 ga watan Junairu, 2020 wanda ya nuna cewa kungiyar ASUU tana barazanar tafiya yajin-aiki.

Hakan na zuwa ne kwanaki 13 bayan malaman jami’an sun amince su janye yajin-aikin da su ka shafe tsawon watanni kusan tara suna yi a kasar.

Dama can ASUU ta bada sharadi cewa muddin gwamnatin tarayya ba ta cika alkawuran da ta dauka ba, ba za su ji kyashin komawa yajin-aiki ba.

KU KARANTA: Bayan watanni 9, ASUU ta janye yajin aiki

Har zuwa yanzu da mu ke samun labari, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba ta kai ga biyan malaman jami’an alawus din da ta yi alkawari ba.

Kusan mako biyu da janye yajin-aiki, The Nation ta ce malaman makaranta ba su ji labarin Naira biliyan 40 da aka ce za a biya su kafin Junairu ba.

Malaman jami’an suna kuma kukan cewa an biya su albashin watanni biyu da aka yi alkawari ne ta manhajar IPPIS, wanda har gobe ake gardama a kai.

Bayan nan gwamnatin tarayya ta dakatar da biyan duk malaman da ba su yi rajista da IPPIS ba.

KU KARANTA: Shugabannin ASUU sun yi zama da Gwamnati a Abuja

ASUU: 2020 ta wuce ba a biya EAA ba, an hana Malamai albashin watan Disamba
Shugabannin ASUU a taro Hoto: www.tvcnews.tv
Asali: Twitter

Jaridar ta ce har yanzu malaman da su ka dawo daga yajin-aiki a ranar 23 ga watan Disamban bara, su na bin gwamnati bashin albashin watanni hudu.

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU ta amince za ta janye yajin aikin da aka kwashe watanni tana yi ne bayan gwamnati ta yi mata alkawura.

Daga cikin alkawuran shi ne za a biya 'yan kungiyar ASUU kudi N70bn, sabanin N65bn da aka ce.

Bayan haka, gwamnatin Muhammadu Buhari ta amince da kara kudin alawus na malaman daga N30bn zuwa N35bn, sannan za a karra kudin gyaran jami'o'i.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel