Kanin Sarkin Daura ya rasu a hatsarin mota

Kanin Sarkin Daura ya rasu a hatsarin mota

- Abin jimami ya samu Masarautar Daura da rashin kanin sarki Alhaji Umar Faruk Umar

- Kanin Sarkin ya rasu ne a wani hatsatin mota da ta afka dashi tare da wasu mutane biyu

-Mataimakin gwamnan jihar Katsina Alh. Mannir Yakubu ya kai ta'aziyya ga masarautar

Alhaji Abdullahi Umar Maitaro, kanin Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar ya rasu. Ya rasu yana da shekaru 57, Daily Trust ta ruwaito.

Maitaro da abokansa biyu sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a kauyen Muduru da ke kan hanyar Katsina zuwa Daura a ranar Lahadin da ta gabata,

Yayin da wani da ya samu raunuka ke karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce motoci biyu, ciki har da na marigayin sun yi karo da juna, yayin da suke kokarin tserewa wani mai tuka a daidaita sahu wanda ba zato ba tsammani ya juyo a gabansu.

KU KARANTA: Abubuwa masu rikitarwa a kasafin kudin 2021

Qanin Sarkin Daura ya rasu a hatsarin mota
Qanin Sarkin Daura ya rasu a hatsarin mota Credit: Daily Trust
Asali: Facebook

Gwamna Aminu Masari, tare da rakiyar mai ba shi shawara na musamman kan ilimi mai zurfi, Dokta Bashir Ruwangodiya, da sauran manyan jami’an gwamnati sun je Daura ranar Litinin don yi wa Sarkin ta’aziyyar rashin da aka yi.

Gwamnan ya kuma ziyarci gidajen sauran mutanen biyu da suka mutu inda ya jajantawa iyalansu.

Hakazalika, Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Alh Mannir Yakubu, wanda kuma shi ne Kwamishinan Aikin Gona, ya jagoranci wata tawaga a ranar Talata don yi wa sarkin ta’aziyya.

KU KARANTA: SERAP ta ƙalubalanci Gwamnatin Najeriya kan Sowore

Har zuwa rasuwarsa, Maitaro ya kasance darekta a Ma’aikatar Aikin Gona ta Jihar Katsina. Ya bar mata daya da yara takwas.

A wani labarin, Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa, ya ce lallai gwamnatin jihar bata biya kowani kudin fansa don sakin daliban makarantar sakandare na kimiyya da ke Kankara ba.

Mista Inuwa ya bayyana a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Talata a Katsina, cewa koda dai an wahala sosai wajen ceto yaran daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su, ba a biya ko sisi a matsayin kudin fansa ba.

Ya ce gwamnatin jihar ta yi amfani da dabaru da dama wajen sakin yaran cewa “a yayin aikata hakan, mun tabbatar da ganin cewar ba a rasa kowani rai ba.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel