Gwamnatin Katsina ta ce lallai bata biya kudin fansar sakin daliban Kankara ba
- Gwamnatin jihar Katsina ta dage kan cewa lallai bata biya yan bindigan da suka yi garkuwa da daliban makarantar sakandare na Kankara kudin fansa ba
- Sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa ya ce ko tantama babu sun sha wuya kafin ceto yaran amma duk da haka basu biya kudi ba
- Yan bindiga a ranar 11 ga watan Disamba, 2020, sun yi awon gaba da kimanin dalibai 344 daga makarantar sakandare ta kimiyya da ke Kankara
Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa, ya ce lallai gwamnatin jihar bata biya kowani kudin fansa don sakin daliban makarantar sakandare na kimiyya da ke Kankara ba.
Mista Inuwa ya bayyana a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Talata a Katsina, cewa koda dai an wahala sosai wajen ceto yaran daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su, ba a biya ko sisi a matsayin kudin fansa ba.
KU KARANTA KUMA: Uba ya tsere yayinda matarsa ta haifi yan hudu a Edo
Ya ce gwamnatin jihar ta yi amfani da dabaru da dama wajen sakin yaran cewa “a yayin aikata hakan, mun tabbatar da ganin cewar ba a rasa kowani rai ba.”
Sakataren gwamnatin ya ce: “sabanin rade-radin da ake yi a wasu bangarori cewa gwamnati ta biya naira miliyan daya don ceto kowani dalibi guda, gwamnatin bata biya ko sisi ba.
“Koda dai, tsarin ya kasance mai tsananin wahala, mun tabbatar da ganin cewa ba a rasa rai ba a yayin aiyukan, muna farin ciki cewa sun dawo cikin koshin lafiya sannan sun sake saduwa da iyayensu.”
Ya yaba da kokarin gwamnatin tarayya ta fuskacin amfani da yan sanda da sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da ceton yaran, jaridar Premium Times ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Ana wata ga wata: Kwamishina ya yi murabus, ya ce gwamnatinsu cike take da rashawa
A ranar 11 ga watan Disamban 2020 ne yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai 344 daga makarantar sakandare na kimiyya da ke garin Kankara a jihar Katsina.
Koda dai yaran sun samu yanci bayan mako guda a tsare, ana ta cece-kuce kan ko an biya wadanda suka yi garkuwa da su kudin fansa.
A wani labarin, yan bindiga sun kashe tsohon sakataren ilimi na karamar hukumar Nasarawa, Malami Salihu sannan suka yi garkuwa da matafiya 20 da ke hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa.
Lamarin ya afku ne a yau Talata, 5 ga watan Janairu da rana a hanyar mungi sharp Conner Buga Gwari, da ke yankin Gadabuke a karamar hukumar Toto.
Yan bindigan sun tsare matafiya 20 a cikin motoci uku sannan suka tisa keyarsu zuwa cikin jeji, jaridar The Nation ta ruwaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng