Karin farashin wutan lantarkin da mukayi ba zai shafi talaka ba, hukumar NERC

Karin farashin wutan lantarkin da mukayi ba zai shafi talaka ba, hukumar NERC

- Gwamnatin shugaba Buhari ta musanta rahoton cewa ta kara farashin wutan lantarki

- Hukumar lura da lantarki ta ce karin da akayi unguwannin masu samun isasshen wuta kawai zai shafa

- A watan Satumban 2020 gwamnatin ta kara farashin lantarki

Hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC, ta karyata rahoton cewa ta kara farashin wutan lantarki na kashi 50 kan abinda kwastamomi ke biya yanzu a fadin tarayya.

NERC a shafinta na Tuwita ta bayyana cewa har yanzu bata bada umurnin kara farashin wuta ba kamar yadda kafafen yada labarai ke watsawa amma unguwannin masu kudi kawai aka karawa.

Hukumar ta ce unguwannin da ke matsayin A, B, C, D da, E aka karawa farashin Kw/hr daga N2.00 zuwa N4.00

"Hukumar (NERC) ta samu labarin wallafe-wallafe da ake yadawa a kafafen yada labarai inda ake fadawa mutane cewa hukumar ta kara farashin wutan lantarki da 50%," hukumar tace.

"Kwastamomin dake matsayin D & E (wadanda ke samun wuta kasa da sa'o'i 12 a rana) ba ayi musu kari ba kuma har yanzu suna jin dadin tallafin gwamnatin tarayya."

"Amma bisa dokar EPRSA, an kara farashin wuta ga masu matsayin A, B, C, D da E daga N2.00 zuwa N4.00 sakamakon hauhawar tattalin arzikin Najeriya."

Read more at: https://www.vanguardngr.com/2021/01/nerc-admits-rates-adjustment-to-n4-per-kwh/?utm_source=dlvr.it&utm_medium=twitter

KARANTA: Karya ne, gwamnatin Buhari ba ta mana tsegumi - Kamfanin Intels ga Atiku

Karya ne, bamu kara farashin wutan lantarki ba, hukumar NERC
Karya ne, bamu kara farashin wutan lantarki ba, hukumar NERC
Asali: UGC

KU KARANTA: Ba mu na niyyar sake Lockdown, Ministan labarai, Lai Mohammed

Watanni hudu da suka gabata, shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin baiwa dukkan yan Najeriya mitan wutan lantarki domin kawar da tsarin da ake kai yanzu na raba 'Bill' na kiyasi.

A takardar da aka saki ranar Laraba, shugaban hukumar lura da wutan lantarki a Najeriya (NERC), James Momoh, ya ce hakazalika shugaba Buhari ya bada umurnin kara farashin wutan.

Amma Momoh yace za'a togaciye "Talakawan" Najeriya daga karin farashin da za'ayi. Shugaban NERC ya ce karin kudin ba zai shafi wadanda ake rabawa 'Bill' na kiyasi ba har yanzu har sai sun samu mita.

Hukumar (NERC), ta sanar cewa za'a fara dabbaka karin farashin wutan lantarki fari daga ranar 1 ga Satumba, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel