Ba mu da niyyar sake Lockdown, Ministan labarai, Lai Mohammed

Ba mu da niyyar sake Lockdown, Ministan labarai, Lai Mohammed

- Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara

- Yayinda wasu jihohi ke sanar da ranakun komawar su makarantu, wasu na tunanin sake kafa dokar kulle

- Gwamnatin tarayya ta yi watsi da maganar sake saka dokar garkame jama'a a gida

Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed, a jiya ya tabbatarwa yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya ba tada niyyar sake kakaba dokar kulle a kasar sakamakon waiwayen korona na biyu.

Ministan wanda yayi jawabi da wani taro a Legas, ya yi kira ga yan Najeriya su bi dokokin da kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar COVID-19 ta gindaya.

Lai Mohammed yace: "Game da maganar sabuwar dokar kulle, ban tunanin gwamnati ta ce zata sake kulle jama'a. Amma gwamnati ba ta jin dadin yadda yan Najeriya ke wa dokokin saka takunkunmin fuska, wanke hannu da bada tazara, rikon sakainar kashi."

"Idan muka ki daina haka, adadin masu kamuwa da cutar zai karu musamman yanzu da aka samu wani sabon irin cutar wacce tafi tsohuwar hadari."

"Gwamnatin tarayya na sane da illar da wani sabon kulle zai yiwa tattalin arziki da rayuwa, amma muna kira ga yan Najeriya su taimakemu, su taimaki kawunansu kuma su taimaki tattalin arziki, ta hanyar bin dokokin COVID-19."

KU KARANTA: Karya ne, gwamnatin Buhari ba ta mana tsegumi - Kamfanin Intels ga Atiku

Ba mu na niyyar sake Lockdown, Ministan labarai, Lai Mohammed
Ba mu na niyyar sake Lockdown, Ministan labarai, Lai Mohammed
Asali: UGC

Mutane 1204 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Litinin, 5 ga watan Junairu 2021, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 91,351 a Najeriya.

Daga cikin mutane sama da 90,000 da suka kamu, an sallami 75,699 yayinda 1318 suka rigamu gidan gaskiya.

Wani sabon nau'in cutar Korona da ya samo asali daga Ingila ya shigo Najeriya makonnin bayan nan.

KU KARANTA: Karya ne, bamu kara farashin wutan lantarki ba, hukumar NERC

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel